Jami’an tsaro a Sokoto sun daura damarar fatattakar ‘yan ta’adda a jihar

0

A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban rundunar soji dake jihar Sokoto Clement Abiade ya sanar wa manema labarai cewa za su hada guiwa da sauran jami’an tsaron dake aiki a jihar domin yin farautar masu tada zaune tsaye a karamar hukumar Rabbah dake jihar Sokoto.

Idan ba a manta ba a ranar 9 ga watan Yuli ne wasu ‘yan ta’ada suka fara wa karamar hukumar inda mutane da dama suka rasa rayukan su.

“Matakan da jami’an tsaro suka dauka sun hada farautar wadannan mutane a kugurmin dazuka Sokoto da wuraren da suke buya a fadin jihar.”

A karshe brigediya Kennedy Udeagbala ya hori jami’an tsaron da su zage damtse wajen ganin sun kamo wadannan mutane dake tada hankular mutane a jihar.

Share.

game da Author