Zan sake fitowa takarar gwamnan jihar Sokoto -Mukhtar Shagari

0

A yau Laraba ne Mukhtari Shagari ya sanar cewa zai fito takaran gwamnan jihar Sokoto.

Shagari ya sanar da haka ne a garin Sokoto zama da ya yi da wasu daga cikin shugabanin jam’iyyar PDP na jihar.

Shagari ya taba zama minista, mataimakin gwamnan jihar Sokoto a 2007, sannan a shekarar 2015 ya fito takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP inda Aminu Tambuwal na jam’iyyar APC ya lashe zaben.

Shagari ya bayyana cewa idan an zabe shi zai bada karfin sa ne wajen inganta fannonin kiwon lafiya, aiyukkan gona, ilimi, ci gaban matasa da samar da sauran ababen more rayuwa.

” Ina da horo kan shugabanci musamman ganin na rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Sokoto na tsawon shekaru takwas sannan a garin nan babu kauyen da ban zaga ba domin haka na fi kowa sanin damuwar mutane da kuma hanyoyin magance wadadannan matsaloli.

Bayan haka jam’iyyar PDP din ta karbi sabbin gungun ‘yan APC da suka canza sheka zuwa jam’iyyar PDP din a jihar.

Share.

game da Author