Hukumar kwastam ta kama mota dankare da katan 498 na maganin Kodin

0

Shugaban hukumar kwastam na jihar Legas Mohammed Uba ya bayyana cewa hukumar ta kama wata babbar mota dankare da kwalaben maganin kodin da suka kai 498.

” A lissafe wadannan kwalayen magungunan za su kai Naira miliyan 199.2. Inji Uba

Uba ya ce sun kama mutane biyu dake hannu wajen shigo da wannan magani.

Ya ce za su danka wadannan mutane da magani ga hukumar (NAFDAC) domin ci gaba da bincike.

Uba ya kuma kara da cewa a watan Yuli hukumar ta kama motoci 141 dankare da wasu kaya da gwamnati ta hana shigowa da su.

” Mun kama wasu a hanyar Ijebu-Ode, wasu kuma a hanyar Awolowo dake Ikeja sannan a lissafe kayan dake cikin wadannan motoci za su kai Naira 1,120,714,338.”

A karshe ya ce buhunan shinkafa 9,504, jarkokin mangyada 436,katan din naman kaji 333,dilar gwanjo 287 da mutane 10 dake da hannu wajen shigo da kayan na tsare a hukumar.

” A yanzu dai wasu cikin mutanen na tsare a ofishin mu sannan wasu sun sami beli.”

Share.

game da Author