An yanke wa wasu masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a jihar Benuwai

0

A yau ne kotun dake Makurdi jihar Benuwai ta yanke wa wasu mazaje biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alkalin kotun Aondover Kakaan ya yanke musu wannan hukunci ne bisa ga shaidu da hujojin da suka tabbatar cewa su wadannan mazaje masu suna Suleiman Goma da Haruna Idi ne suka kashe Alexandra Adeyi limamin darikar cocin Katolika dake karamar hukumar Otukpo a jihar.

” Bisa ga wadannan shaidu da aka gabatar a gaban kotu ya tabbata cewa Suleiman Goma da Haruna Idi mazaunan kauyen Orokam a karamar hukumar Ogbadibo ne suka kashe limamin da taimakon wani Saidu Abdullahi da Aliyu Garba wanda tuni su sun arce.

” Wadannan mutane sun yi garkuwa ne da Alexandra ranar 26 ga watan Afrilu 2016, suka ajiye shi a dajin Okumgaga dake karamar hukumar Otupko sannan suka nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan biyu.

” Hujjoji sun nuna cewa an biya wadannan kudi Naira miliyan 1.5 amma bayan sun karbi kudin sai suka kashe limamin sannan suka jefar da gawar sa a nan dajin.

A karshe Alkali Kakaan yace rundunar ‘yan sandan jihar sun kama Suleiman Goma da Haruna Idi a cikin wannan daji dauke da bindigogi da layu.

Share.

game da Author