Da farko dole duk wani mai kishin kasa a Najeriya ya godewa Allah, da ya samu shugaban kasar da duniya ta yarda da shi, kuma ake ganin ba zai yi halaye irin na wasu a baya da suka wawashe dukiyar kasarsu su ka kai wata kasa don boyewa ba.
Kusan dai labari na uku da ya ke tashe a yanzu haka a kafafen yada labaran kasa akwai batun kudaden da za a dawowa da Najeriya. A cewar hukuma, kudin zai doshi DALA miliyan dari uku da ashirin da biyu ($320). Kuma ba tare da wani jan ciki ba, gwamnatin Buhari ta ga dacewar rarraba wannan kudi kai tsaye zuwa gidajen talakawa dubu Dari uku da biyu, kuma a wannan wata da muke ciki na Yuli za a fara kasafin.

Ba shakka wannan tsari ya yi ma’ana da dacewa. Don kuwa su na baya ba su yi hakan ba, sai yanzu. Kuma dama burin gwamnati baki daya shine a kawo duk wani tsari da zai saukaka tsananin da masu rauni suke ciki.
To sai dai wani hanzari ba gudu ba shine, lamari gami da tsari na rabon kudin gwamnati ga talakawa abu ne mai kunshe da tarin matsaloli da kalubale. Domin an jima ana hakan, kuma bayanai na ci gaba da maimaituwa ba tare da ganin sauyi ba.
Siyasa, Addini da Kabilanci gami da Kusanci na taka rawa sosai wajen tasirantuwar mutanen da za su amshi wannan kudi. Hakan na nufin ko da sun dace ko da akasin haka ne.
A yanzu da APC ta ke mulki, samar gami da hada sunayen mutanen da za su amfana, dole zai fara ne daga Mazabu, kuma shugabannin Mazabun za su taka rawa sosai, wajen yin aringizon mutanen su, domin tsarin nan da hausawa ke cewa da abokin Daka akan sha Gari.
Malaman addini za su iya samun gurbin fada aji, kususan idan suna jikin ‘yan siyasa. Yanda za a iya cewa ai wane dan bangare kaza ne, wane kaza ne. Don haka kar a sa su wane, ai su ne ke zagin gwamnati, kuma suke dariya idan an ce Buhari ba shi da lafiya.
Tasirin kabilanci musamman a wannan lokaci da ake fama da rikicin kabilanci zai kawo matsala sosai. Domin kuwa ko gwamna zai iya bayar da fifiko sosai ko kabilarsa, ko ma yankin da yake tunanin zai samu kuri’unsu. Kun ga an jefi tsuntsu biyu da dutse daya kenan.
Kusanci da alfarma dama wannan ba a magana. Dole za a sha waya da hakilo gami da kai-kawo da kurda-kurda don ganin an antaya sunayen wadanda ake so, ko da kuwa ba su dace a basu kudin ba.
Wasu za su yi tunanin ai ko tsarin nan na daukar aiki na N-power ba matsalar da ta samu, sai kuma akan wannan? Shi wancan tsarin lamari ne na cike takardu, bayanai da tantancewa gami da jarabawa da sauransu. Don haka ko da wani yace zai sa nasa, idan bai yi karatun ba, to tamkar ma yana wasa da wayonsa ne.
Kar na yi surutu mai yawa, ina ganin domin a adana wani abu mai muhimmanci gami da tarihi da za a jima ana tuno wannan abun alkhairi, ina ganin ya kamata ace an yi wani abu na musamman a zahirance da mutane za su amfana.
Gina makarantu, rijiyar burtsatse ko tuka-huta, da su hanya gami da yalwata dakunan zaman jinya da samar da matattarar ruwa(Dam) da manoma za su yi amfani da su, ina ganin za su fi muhimmanci.
Wata kila watan-wata rana za a iya kallon Dam na ruwa ace ai a zamanin Buhari yana mulkin farar hula aka gina abin nan. Haka dai za ana ta bayar da misalai, kamar yanda su Ahmadu Bello suka inganta Arewa.
Amma da yawa idan sun karbi kudin nan, wani ko gida ba zai je da su ba, zai salwantar da su.
Daganan ya ma manta an biya wannan kudi. Kuma abu mafi sa damuwa ma shine, duk lamari na rabon kudi a Najeriya ba ya rabo da cuta da coge. Wasu da yawa za su karbi dubu uku ne zuwa hudu, kuma su kuma gefe su na godiya da cewa Allah Ya saka!
Daga Hassan M. Ringim.
Discussion about this post