1999-2018: Ba a yi gwamnatin ta kai ta Buhari cin hanci da rashawa ba – Atiku

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin da ta fi sauran gwamnatoci baya lalacewa wajen cin hanci da rashawa, tun bayan dawo da mulkin dimokradiyya cikin 1999.

Atiku ya yi wannan furuci ne a garin Abakaliki, a ranar Talatar da ta gabata, yayin da ya ke yi wa dandazon magoya bayan PDP jawabi.

Ya je Ebonyi ne domin kamfen na neman tsaida shi takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyr PDP a zaben 2019 mai zuwa.

Ya ce abin da kawai gwamnatin APC za ta yi tutiya da shi, bai wuce yaki da cin hanci da rashawa ba. Daga nan sai ya kara da cewa, ba hana cin hanci da rashawa kadai ne ayyukan da suka wajaba kan al’umma a yi musu ba.

“Abin da ke faruwa yanzu a cikin kasar nan ya yi muni kwarai. Sai karya dokokin kasa na kundin tsarin mulkin da doka ta gindaya.”

“Kamata ya yi a ce an samu gwmanti mai jawo al’umma a jika, amma ita wannan gwamnati, babu ruwan ta da jawo al’umma a jikin ta.

“ “Ku na sane da kyau babu wani hadin kai a cikin wannan gwamnatin tarayya, saboda gwamnati ve ta wadanda ba su san ma abin da suke yi ba, ba su da kwarewa, sannan kuma ba iyawa suka yi ba.

“Ita ce gwamnatin da ta fi sauran gwamnatocin baya da suka gabata yawan cin hanci da rashawa tun daga kafa sabuwar dimokradiyya a cikin 1999.

“Kada wani ya zo ya yaudare ku da batun yaki da cin hanci da rashawa. Sun fi sauran gwamnatocin baya handama da babakere, tun daga 1999 zuwa yau.

” Da muka hau gwamnati a 1999, ana saida gangar danyen mai a kan $10 ne amma yanzu $70 ne ake siyar wa amma har yanzu ba a ga wani abin azo agani da gwamnatin ta yi ba.

“Ba mu taba samun gwamnatin da marasa aikin yi kuma matasa suka kai muyane har milyan 11q ba, sai sanadiyyar wannan gwamnatin.

Sannan Atiku ya kara da cewa babban dalilin da ya sa suka nemi hadin guiwar jam’iyyun kasar nan su dunkule wuri daya shine don su ga sun fatattaki APC tun daga jihohi zuwa ofishin shugaban kasa.

Ya roki mutanen jihar Ebonyi da su basu goyon baya su cimma wannan buri nasu.

Share.

game da Author