Kasar Faransa ta doke kasar Belgium da ci daya mai ban haushi a wasan cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake bugawa a kasar Rasha.
Dan wasan Barcelona, Umtiti ne ta jefa wa Belgium kwallo dayan da ya makale har karshen wasa.
Kasar Belgium dai tayi kokarin ganin ta ramo wannan kwallo amma ina hakan bai samu ba sai har aka hura tashin wasa.
Yanzu dai za ta buga wasan wanda zai fito a na uku tsakanin ta da wanda aka ci a wasa tsakanin kasar Ingila da Croatia.