Hakallar dala miliyan 40 na ci gaba da kanannade dan’uwan Jonathan a kotu

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yi watsi da karar da dan uwan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan mai suna Robert Azibaola ya kai domin kotun ta kwatar masa hakkin sa daga hannun EFCC.

Mai Shari’a Mojisola Olatroegun ta ce karar da Azibaola ya kai, wani azarbabi ne da kuma cin zarafin kotu, domin tuni EFCC ta shigar da wasu kararraki a kan sa, amma bai tsaya kare kan sa ba, sai kuma ya garzayo kotun ta.

Mai Shari’a ta ce EFCC ta yi abin da doka ta gindaya mata, dangane da binciken Azibaola da ta ke yi.

Shi dai dan uwan na Goodluck Jonathan, ya kai kara ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, inda ya kalubalanci kamawa da tsarewar da jami’an EFCC suka yi masa dangane da zargin yin walle-walle da dala milyan 40.

Korafin da Azibaola ke yi shi ne, EFCC na son ta yi amfani da kusancin sa da Jonathan ne, ta yadda za su makalo sunan Jonathan a cikin shari’ar da ake yi da shi.

ASALIN HARKALLAR DALA MILIYAN 40 DIN

A cikin takardar rantsuwar da Azibaola ya yi a kotu, ta nuna cewa cikin 2012 ne tsohon mai ba shugaban kasa shawara a kan fannin tsaro, Patrick Azazi, ya neme shi da ya zo ya yi amfani da kwarewar sa ya magance matsakar matsalolin hakar man fetur da suka hada da lalata bututun mai da kuma satar mai din shi kan sa.

Daga nan sai a cikin 2014 aka dumbuza dala har naira miliyan 40 a cikin asusun kamfanin Oneplus Holdings Nigeria Limited, a bisa yarjejeniyar cewa za a biya shi kashi 10 bisa dari na wannan uwar kudi.

Sai dai kuma bayan da sabuwar gwamnati ta hau a cikin 2015, sai kwamitin duba kwangiloli ya bada umarnin da a maida wadancan dala milyan 40 daga kamfanin Oneplus Holdings da gaggawa.

Azibaola ya ce daga nan kawai aka tsare shi bayan jami’an tsaro sun karbo takardar umarnin tsare mai laifi daga kotun Majistare, ana zargin sa da yin almubazzaranci.

Ya ce shi dai abin da ya fahimta, magana ce ta al’amarin kacaniyar aiki, ba za a yi saurin kiran ta laifin da tun daga tashin farko a ce za a tsare mutum ba.

Daga nan sai ya nemi kotu ta hana jami’an EFCC sake tsare shi ko bincikar sa ko cin zarafin sa.

BA’ASI DAGA BAKIN EFCC A KOTU

A nata bangaren, lauyan EFCC mai suna Idris Mohammed ya rattaba ta sa rubutacciyar rantsuwa a gaban mai shari’a cewa, can wani lokaci a cikin watan Nuwamba, 2015, sun samu rahoton sirri wanda ya tabbatar musu da cewa akwai wata harkallar kwangila tsakanin Azibaola, kamfanin sa da ma wasu, wadda Sambo Dasuki ya bayar.

EFCC ta ce kwamitin da aka sa ya binciki kwangilar makamai ne da aka gudanar daga 2007 zuwa 2015, ya gano dabakalar.

GIRIBTUN KWANGILOLIN MAKAMAI

Wannan kwamiti ya gano a tsakanin 2012 zuwa Maris, 2015, Dasuki ya bayar da kwangilolin makamai na naira biliyan 2.2, dala miliyan 1.7, fam milyan 9.9.

EFCC ba a nan kwangilolin suka tsaya ba, Dasuki ya kuja umarci Babban Bankin Najeriya da ya bai wa kamfanin Tunji Adeyemi &Co tsabar kudi naira milyan 650, a matsayin biyan kudin wani gida mai lamba 2245 a unguwar masu hannu da shuni, Maitama, Abuja.

To wadannan kudaden an yi wannan ya karba ya mika wa wancan, har a karshe dai suka kai hannun Azibaola.

EFCC ta ci gaba da bayyana wa kotu dalilin ta na damke Azibaola, cewa da umarnin Sambo Dasuki ne Babban Bankin CBN ya bai wa Oneplus Holdings Limited dala milyan 40 da nufin sayo kayan fama da makamai ga Sojojin Musamman na Najeriya.

WALLE-WALLE DA DALA MILIYAN 40

EFCC ta ce wa kotu Azibaola ya karbi dala milyan 40 da aka zuba a asusun kamfanin sa Oneplus Holdings ba tare da ko fallen takarda daya mai nuna wata yarjejeniyar bayarwa da karbar kwangila ba.

Bugu da kari, EFCC ta ci gaba da zayyana wa Mai Shari’a Mojisola cewa Azibaola ya rika kamfatar kudaden nan ya na balle-bushasha da cin-duniyarsa-da-tsinke, tare da tuttura kudaden ga wasu ana dabdala, ta hanyar kamfanin matar sa Stella Robert da jami’in da ke kular masa da kudade, mai suna Amobi Agum.

JERIN WADANDA SUKA CI MORIYAR WATANDAR AZIBAOLA

Maciya kudaden su na da yawa. Akwai Dike Ndubuisi da ya karbi dala milyan 7.5 a ranar 17 Ga Oktoba, 2014 sai kuma ya kara karbar naira bilyan 1.34 a ranar 27 Ga Janairu, 2015.

EFCC ta ce Azibaola da matar sa sun kimshe wata dala milyan 1.5 a cikin asusun Reya Telecommunications Limited, daga can kuma aka sake tura kudaden cikin asusun NETSPACE Telecommunications.

An kara cirar dala milyan 4.3 aka boye cikin asusun Reya Telecommunications da Jorgenson.

An kuma tura wasu dala miliyan 2 a cikin asusun wani mai suna Kamaludeen Dahiru.

Sai kuma Mangrovetech aka tura masa naira bilyan 2.5, wanda shi din ma EFCC ta ce ta gano mallakar Azibaola ne, amma yanzu sun canja masa suna zuwa Kakatar Ce Limited.

EFCC ta shaida wa kotu cewa sun sha gayyatar Azibaola ya je ya yi bayani, amma ya yi kunnen-uwar-shegu da hukumar, sai ya rika neman kamun-kafa nan da can. A karshe da ya gaji da wasan-buya, sai ya kai kan sa saboda ya san an rigaya an kure masa gudu, za a buga tandar neman sa ruwa a jallo.

Share.

game da Author