Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa ruwa da iska mai karfi ya haifar da mutuwar mutum daya da kuma lalata gidaje akalla 100 a Daura, jihar Katsina.
Baya ga wannan, an kai mutane hudu zuwa asibiti, bayan da irin wannan ruwa da iska ya kori mutane 600 daga muhallin su a yankin.
Wannan bala’i ya afku ne bayan da aka shafe kimanin awa takwas ana kwara ruwan sama kamar da bakin kwarya tun daga ranar Lahadi da yamma.
Daraktan Ilimi, Jin Dadi da Walwala na Daura, Abubakar Mashi ne ya kewaya da Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa, NEMA domin tantance wuraren da abin ya shafa.
Ya kuma bayyana cewa mutanen yankin sun tafka babbar asarar dukiyoyin su sanadiyyar barnar da ruwan ya yi musu.
Jami’an gwamnati da dama da suka je wurin sun ce za a kai musu daukin gaggawa.
Discussion about this post