Dalung ya umarci Shugaban Kwallon Kafa, Pinnick ya sauka

0

Mako daya bayan tawagar jagororin Kungiyar Kwallon Kafar Najeriya da ‘yan wasa sun dawo daga gasar cin Kofin Duniya daga Rasha, Ministan Wasanni Solomon Dalung ya umarci Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa, Amaju Pinnick da ya gaggauta sauka daga kan mukamin sa.

Wannan umarni kuwa na cikin wata wasika da Ministan ya aika wa Shugaban Hukumar Kwallon Kafa na Kasa, wadda Babban Hadimin Ministan, Nneka Ikem Anibeze ya sa wa hannu, Dalung ya nusasshe da Pinnick umarnin da kotu ta bayar, inda ta jingine zaben ranar 30 Ga Satumba, 2014, wanda shi ne ya kai Pinnick din zama shugaban hukumar ta kwallon Najeriya.

Dalung ya kara da cewa umarnin da ya bayar ya biyo tunatarwar da Antoni Janar na Tarayya ya yi wa Ma’aikatar Wasanni cewa ta sanar da Pinnick ya gaggauta bin umarnin kotu.

A kan haka ne Minista Dalung ya ce umarnin kotu ne shi ma ya bi da aka ce ya umarci Pinnick ya sauka.

“Wannan umarni ne daga kotu, ba daga Dalung ba. Ba zan so haka kawai dalilin wani a tura ni kurkukun Kuje ba, saboda kin bin umarnin kotu.

“Don haka ina umartar ka da ka bi umarnin kotu na ranar 5 Ga Yuni, 2018, ka sauka. Kamar yadda ni ma aka ba ni umarni aka ce na sanar da kai umarni daga kotu, ka sauka.”

Tuni dai ita kuma FIFA ta rubuto cewa ita ba ta san da wasu shugabannin hukumar kwallon kafar Najeriya, sai Amaju Pinnick da sauran mukarraban sa.

Share.

game da Author