Abin da Buhari ke nufi da ya da ce akwai hannun Libya a rikicin makiyaya da manona

0

Gwamatin Tarayya ta dora laifin kashe-kashen Fulani makiyaya da manoma a kan sakacin fantsamar makamai daga kasar Libya zuwa cikin Najeriya, ta hanyar zirga-zirga daga Sahara.

Ministan Tsaro Mansir Dan-Ali ne ya bayyana haka a wani taron ganawa da jama’a dangane da matsalar rikicin-makiyaya da manoma.

An gudanar da taron a ranar Alhamis a Abuja.

Ya bayyana cewa abin da Buhari ke nufi da ya yi maganar Libya a watannin baya, ya na nufin yadda aka rika shigo da makamai daga kasar Libya, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka masu yawa.

Ya ce gwamnati ta kafa kwamitin kuma ta dora wa Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa aikin sake gina kauyukan da rikici ya ritsa da su a jihar Benuwai, kuma tabbatar kauyukan ba su yi nisa da junan su ba.

Sai dai kuma ya i korafin cewa sojojin kasar nan ba su da yawan da za a ce sun tsare kowane kauye da ke cikin yankin Arewa ta Tsakiya domin su hana kashe-kashe.

Taron wanda Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya shirya shi, ya samun halartar Ministan Tsaro Dan-Ali, Ministan Cikin Gida Janar Abdulrahman Dambazau da kuma Ministan Gona Audu Ogbe.

Shi ma Dambazau ya kara jaddada cewa makaman da aka shiga da su daga Libya ne suka kara munin kashe-kashen Fulani makiyaya da manoma, ba ma a Najeriya kadai ba, har da sauran yankin Afrika ta Yamma da ke cikin yankin Sahara.

Share.

game da Author