Gwamna Shettima ya tuhumi kwamishinan da ya raba wa matasa tallafin kayan shushana

0

Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, ya aika wa Kwamishinan Ilmi Mai Zurfi na jihar, Usman Babawo takardar tuhuma, saboda kunyata jihar da ya yi, inda ya raba wa yara matasa kayan jarin wankin takalmi da buhunan lemon zaki domin su ja jari.

Babawo dai ya raba kayan ne ga matasan Karamar Hukumar Gwoza, inda yakin Boko Haram ya yi illa sosai a jihar Borno.

Rahotanni da dama sun tabbatar da cewa kwamishinan ya yi haka ne da nufin inganta rayuwar matasan yankin, a gefe daya kuma ya na neman kujerar Majalisar Tarayya ce ta Karamar Hukumar Gwoza.

Hotunan tarkacen akwakun wanke takalma da buhunan lemon zaki sun cika soshiyal midiya, wanda hakan ya janyo wa gwamnatin jihar da ma gwamnonin Arewa tsangwama da muzantawa ainun.

Ganin yadda gwamnan ya harzuka ne, ya sa har ya ja hankalin kwamishinan, wanda ya ce ya kunyata gwamnatin jihar Barno da gwamnan kan sa. Haka dai wani jami’in gwamnatin jihar ya shaida wa ‘yan jarida.

Daga nan kuma sai majiyar ta ci gaba da shaida cewa, gwamnan ya tunatar da kwamishinan irin namijin kokarin da gwamnatin sa ta yi wajen inganta rayuwar matasa maza da mata.

Sai dai kuma yayin da wasu da dama ke tofar da yawun Allah-tsine dangane da abin da suke ganin rashin maida hankali ne ga inganta rayuwar matasa, wasu kuma na ganin hakan da kwamishina Babawo ya yi ba karamin taimako ba ne ga yaran.

Wani mai sharhin siyasa da al’amurran yau da kullum, mai suna Dakta Aminu Gamawa, ya bayyana cewa, bai kamata ana kushe namijin kokarin da kwamishinan ya yi ba.

Ya yi tsinkayen cewa wadannan yara matasa ba ilmi gare su ba, don haka babu yadda za a yi a dauke su a ba s u wani aikin haro na samar wa kan su sana’o’i irin na zamani da ake amfani da ilmi wajen cin moriyar su.

Ya ce da ya ke ba ilmi gare su ba, kuma ga talauci, hakan da aka yi musu daidai da rayuwar da suke a cikin ta, ba laifi ba ne, domin duk ta inda za a kalli tallafin dai ya inganta su ko da yaya.

Daga nan sai ya ce da yawa daga cikin matasa masu saida lemun zaki a kasuwanni fa, ribar da suke samu a wata ta zarce albashin wasu ma’aikatan ngwamnati nesa ba kusa ba.

Ya ce yara ne su na zaman banza ba su da komai. Shin so ake yi sai sun kai ga afkawa cikin muggan laifuka sannan kuma a dawo ana zagin su?

Share.

game da Author