YAJIN AIKI: JOHESU ta yi kira da a tsige ministan Kiwon Lafiya, Isaac Adewole

0

Kungiyar ma’aikatan jinya (JOHESU) ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta tsige ministan kiwon lafiya Isaac Adewole saboda nuna halin ko in kula da kokarin ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ke yi kusan wata daya kenan.

Idan ba a manta ba kungiyar JOHESU ta fara yajin aiki na gama gari ne ranar 17 ga watan Afrilu a dalilin rashin biyan bukatun su da gwamnati ta kiyi.

Yanzu dai yajin aikin ya yi muni domin yawancin jihohi da kananan hukumomin kasar nan sun bi sahu.

Ita ko kungiyar likitocin kasar nan cewa ta yi bata ga dalilin shigar kungiyar yajin aiki ba cewa duk abinda suke so an biya musu. NMA ta ce muddun gwamnati ta biya musu bukatun da suke nema a hannun su to tabbas suma za su fara yajin aikin.

Bayan haka a makon da ta gabata ne shugaban kungiyar JOHESU Biobelemoye Josiah ya zargi ministan kiwon lafiya Adewole da ministan kwadago Chris Ngige da nuna halin ko in kula da abinda suke bukata a wajen gwamnati da kuma rashin nuna damuwa kan yajin aikin.

Kungiyar sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsige ministan kiwon lafiya domin ya kasa gano bakin zaren.

Share.

game da Author