Tun bayan rantsar da sabuwar majalisar dattawa ne a 2015, wasu daga cikin sanatocin da aka zaba ke ta sintirin yau suna wannan kotu gobe suna wancan ko kuma jigilar hukumar EFCC.
1 – BUKOLA SARAKI
Sanata Bukola Saraki, wanda shine shugaban majalisar dattawa ya fi kowa ganin tasko.
A farko-farkon zaman sa shugaban majalisa ya dinga sintirin kotun kula da da’ar ma’aikata domin amsa tambayoyi kan tuhumar sa da ake yi na boye wasu kadarorin sa da kin fadin su cikin bayanan abubuwan da ya mallaka kafin ya zama shugaban majalisar.
2 – Ike Ekweremadu
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, ya afka cikin kamayamayar da ta yi sanadiyyar zaman Saraki shugaban majalisa inda aka zarge shi tare da akawun majalisar Efuturin wajen canza wani sashe na dokar majalisar domin ba Saraki dama ya zama shugaban majalisar.
Bayan haka kuma ana zargin sa da mallakar wasu kadarori a kasahen Amurka, Britaniya, Dubai, da gwamnati ta rubuta ta na so a kwato su, su zama na kasa.
3 – Dino Melaye
Sanata Dino Melaye ko, zargin sa akeyi da labta wa ‘yan sanda karya cewa wai an nemi a kashe shi bayan ba haka bane, sannan an kama shi da laifin ba wasu gungun matasa makamai da ya hada da bindigogi, da yanzu haka yake fuskantar wannan shari’ar a Kotu.
4 – Peter Nwaboshi
Sanata Peter Nwaboshi daga jihar Delta na fuskantar shari’a ne a kotu bayan hukumar EFCC ta doka shi a gaban kuliya tana tuhumar sa da waske wa da naira miliyan 322. An bashi beli ne bayan dan zama da yayi a firzin.
5 – Kashamu Buruji
Shi ko Sanata Kashamu Buruji ya dade yana dumulmule a kotunan Najeriya. Bayan tuhumar sa da yin fasakwaurin muggan kwayoyi da akeyi da har yasa aka nemi da ya kai kan sa kasar Amurka domin amsa tambayoyi a akai.
6 – Ahmed Yerima
Shima Sanata Ahmed Sani Yerima ya tsaya gaban hukuma ICPC in da hukumar ta tuhumasa da wawushe kudi da ya kai naira biliyan 1 na gina dam a jihar Zamfara. sai dai an dakatar da ci gaba da sauraren wannan kara ne bayan wanda ya shigar ya kasa bada kwararan hujjoji.
7 – David Mark
Tsohon Shugaban majalisar dattawa David Mark, ya bayyana a gaban hukumar EFCC in da a ka tuhumesa da hannu dumu-dumu a batar wasu kudade har naira biliyan 2 da aka saka a asusun majalisar kasa lokacin zaben 2015.
8 – Stella Oduah
Tsohuwar ministan sufurin jiragen sama, Stella Oduah, ta gurfana a gaban hukumar EFCC ita ma kan zargin waske wa da sama da naira biliya 3 cikin naira biliyan 9 da aka samar don gyaran filayen jiragen saman Najeriya.
9 – Danjuma Goje
Sanata Danjuma Goje na fuskantar tambayoyi bayan zarginsa da hukumar EFCC tayi na yin harkallar kudade har naira biliyan 25, kudin jihar Gombe a lokacin da yake gwamnan jihar a kwangillolin karya.
10 – Adamu Abdullahi
Sanata Adamu Abdullahi, EFCC na tuhumar sa kan harkallar wasu kudade da ya kai naira biliyan 15 tun shekarar 2010.
11 – AbdulAziz Nyako
EFCC na tuhumar Nyako da hannu a badakalar bacewa naira biliyan 29 kudin wasu ayyuka a jihar Adamawa lokacin mahaifin sa na gwamnan jihar.
12 – Joshua Dariye
Ana tuhumar Dariya ne kan bacewar wasu kudade da yakai naira biliyan 1 kudin tallafi na raya kasa.
13 – Jona Jang
Sanata Jonah Jang , bai dade da fitowa daga gidan maza ba kan zargin wawushe samam da naira biliyan 6 , kudin mutanen jihar Filato.