Shugaban hukumar zabe na jihar Nasarawa, Henry Omaku, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ce ta lashe zaben kujerun kansiloli 147 da na shugabannin kananan hukumomi 13 a zaben da aka yi jiya a fadin jihar.
Ko da yake jam’iyyar PDP bata shiga zaben ba, jam’iyyu 21 suka fafata a zaben sai dai kash, ko kujera daya babu jam’iyyar da ta samu koda ko ta kansila ce.
Kaf APC ce ta lashe zaben a jihar.
Wasu daga cikin korafin da APGA da PDP suka yi shine wai suna da tabbacin cewa shugaban hukumar zaben na jihar dan jam’iyyar APC ne.
Discussion about this post