Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa bai ga dalilin da zai sa ya dinga yi wa shugaban kasa izgilanci ba ko kuma ya na sukar sa don yana dan jam’iyyar adawa, PDP.
Umahi ya ce a tarbiyar da ya samu na rayuwa, an karantar dashi yadda zai rika girmama na gaba da shi ne musamman shugaban sa, ba sukar sa ba.
” Duk wani kushe shugaba Buhari da za a yi na bari wa jam’iyya ta, saboda shi Buhari ba Allah bane. Zai yiwu bai yi yadda ake so ba 100 bisa 100,wannan ba aiki na bane in yi ta kushe shi. Ni nawa sai dai in maida hankali kan abin da na sa a gaba wato ganin ci gaban jiha ta.
” Sannan kuma ni bazan ce zan binciki gwamnatin baya ba, aiki na shine abin da na samu in maida hankali in yi wa mutanen jiha ta aiki.
Ya ce maganan cin hanci da rashawa kuwa, ba jam’iyya bace dungurugum ta shafa, wannan abu ne da ya shafi wanda yayi, idan har jam’iyya mai mulki ta karbi irin wadannan mutane, to kaga ita ma an goga mata kashin kenan.
” Babu wani da ke jam’iyyar adawa da zai iya ja dani a zabe a jihar nan. Wasu da yawa suna cewa suna wa Buhari aiki ne, amma a gaskiya angulu ne da kan zabo, rufa-rufa suke yi. Sannan dukkan su ma ko gidan zama basu dashi a Jihar.
” Su sani cewa duk wanda ya ce zai yi amfani da karfin gwamnati mai mulki daga Abuja ya juya zabe a jihar nan to ya saurari abin da matasa suka ce,” Ka rubuta sakamakon zabe na murdiya, sannan kuma ka rubuta yadda za a raba gadon ka.”
Gwamna Umahi ya bayyana haka ne a garin Abakaliki a taro da yayi manema labarai domin bukin ranar dimokradiyya.