Ina nan a Jam’iyyar APC daram dam – Okorocha

0

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya karyata rade-radin da ake yi ana cewa zai fice daga jam’iyyar APC ya ko ma jam’iyyar sa ta ainihi, APGA.

Sakataren Yada Labarai na gwamnan, Sam Onwuemeodo ne ya ce zantukan duk karairayi da surutan magauta ne kawai.

Ya ce har yanzu Okorocha ne ke rike da akalar jam’iyyar APC a jihar Imo ba wani ko wasu ba.

An rika rade-radin cewa gwamnan zai fice daga jam’iyyar APC bayan da ya rasa kusan akasarin mutanen sa ba su samu damar samun mukamai a zabukan shugabannin mazabu da aka gudanar ba.

Rade-radin sun kara ruruwa bayan da aka ruwaito cewa ya ce zai iya cin zabe a jihar Imo ko a karkashin APGA, ba ma sai ya goya cikin jam’iyyar APC ba.

Bangaren magoya bayan gwamnan ba su samu nasarar hawa mukaman jam’iyya a zabukan shugabannin mazabu, kananan hukumomi da shugabannin jam’iyya na jihar Imo ba.

Zaben da aka yi na shugabannin jiha Imo dai Okorocha ya yi tir da shi, domin a cewar sa, akwai sammace daga kotu wanda ta ce kada a gudanar da zabe har sai kotun ta warware rikicin jam’iyyar wanda ke a gaban ta tukunna.

Share.

game da Author