Ana ta ci gaba da samun rabuwar kawuna a cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, tun bayan zabukan shugabanni da aka gudanar na jam’iyyar.
A jihar dai magoya bayan APC da ke bangaren Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed sun maka APC bangaren Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki kotun domin neman hakkin da suka cec an danne musu.
APC dai ta rabe gida biyu ko ma uku a jihar Kwara, inda bangaren magoya bayan Lai Mohammed suka kalubalanci zaben shugabannin jiha na jam’iyyar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Dukkan bangarorin biyu sun gudanar da na su zaben daban-daban a ranar Asabar din da ta gabata.
A cikin takardar karar da aka shigar jiya Litinin, 21, Mayu, 2019, bangaren na Lai Mohammed sun roki kotu da ta hana shugaban jam’iyya John Oyegun da Mai-Mala Buni amincewa da zaben da bangaren Saraki suka yi.
Har ila yau takardar karar na so kada a sake a amince da shugaban jam’iyyar da bangaren Saraki ya ce shi ne ya ci zabe.
Bunmi Olusona da Toyin Ayinla ne suka shigar da karar, inda suka hada har da Oyegun, Buni da Fulani duk suka maka su kotu.
Sun ce sun kai karar ne saboda bangaren Saraki sun balle sun yi na su zaben daban, kuma har suna bugun kirjin cewa babu wanda ya isa ya taka musu burki, ko ya haramta zaben da suka yi.
Discussion about this post