2019: Abin da ya kai Gwamna Dickson ga El-Rufai da Makarfi

0

Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya kai ziyara ga takwaran sa na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, inda suka yi ganawar sirri, a matsayin wani rangadin fadin kasar nan da Dickson ke yi.

Bayan ya gana da gwamnan, daga nan kuma ya zarce suka gana da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi.

Kakakin yada labaran gwamna Dickson ya bayyana cewa ya na rangadin fadin kasar nan ne domin ya nemi hadin kai kan muradin da wasu ke yi a sake fasalin kasar nan.

Ya na neman hadin kai ne daga gwamnoni da kuma shugabanni da sauran masu fada a ji na jihohi daban-daban.

El-Rufai shi ne shugaban kwamitin tattauna batun sake fasalin kasar nan da jam’iyyar APC ta kafa.

Sanarwar ta ce gwamna Dickson na cike da kishin kasar nan da kuma son kasancewar ta dunkulalliya daya a cikin zaman lafiya da lumana.

Sai dai ya na mai nuna cewa kasar za ta fi kara samun ci gaba da yalwar arziki idan aka koma tsarin fifita shiyya a karkashin fedaraliyya.

Yayin da ya ke kira da a bada hadin kai ga tsarin, Dickson ya kara da cewa tsarin sake fasalinn kasa zai bai wa jihohi mallakar mafi yawan kaso daga albarkatun da ke shimfide cikin kasar su.

Daga nan kuma ya je ya gana da Makarfi, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su yin taka-tsantsan da kuma kaffa-kaffa wajen nuna karfi ko kama-karya a zaben 2019.

Dickson ya kuma roki daukacin dukkan ‘yan siyasa da su da ‘yan Najeriya gaba daya su bayar da fifiko wajen tabbatar da an gudanar da zane mai adalci a fadin kasar nan.

Ya ce kamata ya yi ‘yan siyasa su rika girmama juna da mutunta juna, domin kamar yadda ya jaddada, a karshe dai duk gida daya ake kuma ‘yan uwan juna ne.

Dangane da zabukan kananan hukumonin Kaduna da za a sake gudanar da wasu, ya roki a guji duk wani abu da zai kawo barkewar tashe-tashen hankula a jihar.

A karshe ya jinjina wa PDP ta jhar Kaduna dangane da yadda ta samu nasarar cin kananan hukumomi hudu daga cikin 18 din da aka bayyana sakamakon su.

Share.

game da Author