Baya ga rahotannin da PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo a jiya Lahadi, inda ta bada labarin irin tarangahumar da ta faru yayin zabukan shugabannin shiyyoyi na jam’iyyar APC, a yanzu kuma wasu rahotanni na ci gaba da kara bayyana cewa ana ci gaba da samu baraka a cikin jam’iyya, har abin na neman ya ta’azzara.
JIHAR KANO: A jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso bai halarci taron gangamin zaben a mazabar sa ta Madobi ba, kamar yadda Buhari ya je ta sa Mazabar a Daura ba.
Haka shi ma Maitaimakin Gwamnan Jihar Kano, Hafiz Abubakar, bai je mazabar sa ta Mandawari da ke cikin birnin Kano ba. Sannan kuma dan uwan sa da ke shugabancin jam’iyyar, bas hi aka zaba ba, an zabi wani mai suna Salisu Sani.
Wani abu da ya kara tabbatar da yagewar rigar APC zuwa gida biyu a Kano, shi ne yadda mabiya Kwankwasiyya su ka gudanar da na su zaben a mazabu 484 na jihar da ban da na APC Gandujiyya.
Kakakin Sanata Kwankwaso, Rabi Spikin, ta shaida cewa sun gudanar da na su zaben lami lafiya, kuma za su tattara sakamakon gaba daya su kai wa ofishin jam’iyyar APC na kasa baki daya.
APC dai na cikin fargabar gudun kada mabiya Kwankwasiyya su yi wa jam’iyyar ‘anti-party’, wato su zabi duk ma wani wanda wata jam’iyya mai karfi ta tsaida maimakon Ganduje da Buhari.
Sai dai kuma Spikin ta yi tir da kafafen yada labarai cewa ba su bi mazabu-mazabu sun dauko rahoton yadda Kwankwasiyya ta gudanar da na ta zaben ba.
JIHAR KATSINA: A jihar Katsina tuni wasu hasalallu, bayan yin tir da abin da suka kira dauki-dora da aka yi, sun kuma tabbatar da cewa ba za su taba yarda a tafi a haka ba, domin karfa-karfar da aka yi a jihar, ba zabe ba ne.
Abdulkadir Damale da Hassan Isah, sun bayyana cewa za su garzaya kotu, domin duk mai kishin jihar Katsina ya tabbatar da cewa ba a yi zabe a jihar ba, sai karyar canji kawai a baki.
Damale ya yi zargin cewa an kwashe jami’an hukumar zabe da suka je sa-ido, aka boye su a cikin gidan gwamnatin jihar Katsina, sannan aka ba su sunayen da aka ga dama, aka ce wai su ne suka ci zabe.
PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da samun rudani a wurare da dama a jihar. Majiya kwakkwara ta tabbatar da cewa a Barkiya da ke cikin karamar hukumar Kurfi, ba a yi zabe ba. Akwai kuma masu cewa ba a yi zabe a karamar hukumar ba dungurugum.
A karamar hukumar Kurfi, majiya ta ce akwai sabani tsakanin ‘yan APC na asali da kuma wasu da su ka yi taka-haye su ka tsallaka katangar PDP su dira APC.
Ganau ba jiyau ba, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa a garin Banye da ke cikin Karamar Hukumar Charanci, a kan idon sa aka rika jibgar wani jami’in zabe, don ya nemi ya hana a yi yadda wasu ke so a yi.
“Ni dai ina daga nesa, ban matsa kusa da su ba. Ina ganin ana dukan sa, har aka kekketa masa riga. Da kyar ‘yan sanda suka ceci shi, da sai abin ya yi muni kwarai.” Inji majiyar mu.