SUNAYE: Daliban Makarantar Yaye Manyan Jami’an ’Yan Sanda hudu da suka rasu a hadarin titin Kano zuwa Zariya

0

Jiya Lahadi ne wasu daliban Makarantar Yaye Manyan Jami’an ‘Yan Sanda ta Wudil, su ka hadu a ajalin su, sakamakon mummunan hadarin da ya ritsa da su.

Baya ga su hudun kuma, akwai wasu fasinjoji biyu da su ma aka yi asarar rayukan na su.

Kwamandan Shiyyar Zaria na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, Muktar Zubairu, ya shaida cewa hadarin ya faru ne yayin da motoci biyu, daya kirar J5, daya kuma kirar Golf su ka hadu, inda nan take suka kama da wuta.

Ya ce abin ya faru ne a daidai Kwanar Likoro, kusa da Tashar Yari. Ya ce motocin biyu taho-mu-gama su ka yi, wanda shi ne dalilin kamawar motocin da wuta a take.

Sai dai kuma ya danganta afkuwar hadarin da aikin gyaran titin Zaria zuwa Kano da ake kan yi, wanda hakan ya tilasta motoci masu tafiya da masu dawowa ke bi ta bangaren hannun titi daya.

Ya ce wannan kuwa ya sha haddasa yawaitar hadurra sosai.

Daga nan sai ya lissafa wasu dalilai da ka iya haddasa yawaitar hadurra a kan titin, da y ace sun hada da: gudun-wuce-sa’a, wuce motar da ke gaban ka a inda bai dace ka wuce ta ba, tayoyi marasa nagari, tukin ganganci, amsa kiran waya ga direba da kuma kin bin dukkan ka’idojin tuki a kan bannan titi.

Wakilin ‘yan sanda Rufa’i Suleiman, ya bayyana cewa dukkan masu kwas din horon manyan jami’an dan sanda su hudu din, su na cikin shekarar karatun su ta karshe ne a Police Academy, Wudil.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa daga cikin masu koyon aikin zaratan ‘yan sandan su hudu, har da mace daya, mai suna Aisha Bello.

Aisha ita ce Shugabar Kungiyar Mata Musulmi (MSSN), ta Police Academy, Wudil.

Wadanda hadarin ya ritsa da su din, sun hada da: Cadet ASP Aisha Bello (Sociology); Cadet ASP Abdulrahman Dari (Physics); Cadet ASP AM Bello (Physics); Cadet ASP Yusuf Shehu (Sociology); Cadet ASP Rufai Dikko (Computer Science) da kuma; Cadet ASP El-Yaqub.

Share.

game da Author