Shugaba Muhammadu Buhari, ya gana da Gwamna Abdul’aziz Yari na Zamfara da Rochas Okorocha Jihar Imo, inda su ka sanar da shi irin yadda zabukan shugabannin mazabun jam’iyyar APC ya gudana a fadin kasar nan a ranar Asabar.
Bayan ganawar ta su, Okorocha ya shaida wa manema labarai cewa sun sanar da shugaban irin yadda ta kaya a yayin zabukan da jam’iyyar APC da shirya a fadin mazabun kasar nan baki dya.
Ya ce Buhari ya bata fuska sosai tare da rashin jin dadi, jin yadda a wasu jihohi ba a gudanar da zaben ya tafi daidai ba. Ya ce Buhari bai ji dadin irin halayyar da wasu ‘yan jam’iyyyar APC su ka nuna a wurin zabukan ba.
Gwamna Okorocha, ya ce Shugaba Buahari ya ce za a tari gaba, domin a magance sake faruwar haka.
A na sa bangaren, shi ma Okorocha ya bayyana cewa, “mun yi tunanin za a nuna da’a da tattako irin na tsarin dimokradiyya. Domin halayya irin ta siyasar sace akwatin zabe a tsere da shi, satar sakamakon zabe duk halayya ce irin ta siyasar da can baya.”
Sai dai shi kuma Gwamna Yari, ya yaba da yadda zaben ya wakana a Shiyyar Arewa-maso-Yamma, har ma ya kara da cewa: “Ya kamata ku sani a tsarin dimokradiyya ba za ka yi tunanin samu ko aiwatar da komai daidai-wa-daida ba.”