Bayan tallata wa duniya da labaran jaridun kasar nan suka yi cewa jam’iyyar APC za ta wanke Ali Modu Sherrif a hedikwatar jam’iyyar yau cewa zai canza sheka daga PDP zuwa APC hakan dai bai yiwu ba.
Bayan manema labarai sun taru a ofishin jam’iyyar dake Abuja, tun da asubahin farko zuwa karfe 12 na rana da aka ce zai iso hedikatar jam’iyyar domin ganawa da shugabannin APC da sauran ‘ya’yan jam’iyyar, karshen ta dai sai dai kowa tattara komatsan sa yayi kara gaba.
Daga baya sai kakakin jam’iyyar Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ba a hedikwatar jam’iyyar ne ake ba da katin zama dan jam’iyya ba.
” Duk mai bukatar ya shigo jam’iyyar APC, a mazabar sa zai karbi katin shiga ba hedikwatar jam’iyyar ba.”