Darektan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Lawrence Ojabo ya bayyana cewa gwamnati ta kafa kwamiti domin duba yadda za a kawo karshen yajin aikin da kungiyar ma’aikatan asibitocin kasar nan suka fara makonni biyu kenan.
Ojabo ya fadi haka ne a Abuja sannan ya kara da cewa tuni kwamitin ta fara zama da ‘yan kungiyar.
Idan ba a manta ba a makon da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta yi wa kungiyar JOHESU barazanar dakatar da albashin su idan har basu janye yajin aikin da suka fara ba.
A halin yanzu kungiyar ta lashi takobin ci gaba da yajin aiki cewa barazanar da gwamnati take yi cewa baza ta biya ma’aikatan kungiyar albashi ba, ba zai tsorata mambobin kungiyar ba.
A tsokacin da ya yi ranar Juma’a shugaban kungiyar Biobelemoye Josiah ya bayyana cewa ‘‘Muna so mutanen kasar nan su fahimci irin rashin nuna adalci da nuna wariya da shugabanin ma’aikatar kiwon lafiya ke yi mana da likitoci sannan duk da haka gwamnati ta na mara musu baya domin har barazana take yi mana na hana mu albashin mu idan ba mu dakatar da yajin aikin ba.
Bayan haka Ojoba ya tabbatar da cewa ma’aikatar asibitocin gwamnati za su ci gaba da aiyukkan su yadda ya kamata sannan y ace gwamnati ta zuba jami’an tsaro domin ganin haka ta faru.
A karshe mataimakin shugaban kungiyar na kasa Ogbonna Chimela yace babu sauran zama da ke tsakanin su da gwamnatin tarayya sai dai kawai idan za a tattauna yaushe za ta biya su bashin albashin su da suke bi kawai.