A dalilin rashin zaman lafiya da mazauna kauyen Bena dake karamar hukumar Danko/Wasagu jihar Kebbi rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wasu ‘yan ta’adda 11 a garuruwan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Kabiru bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kashe mutane biyar a a kauyen Bena da ke da iyaka da jihar Zamfara.
” Dama maharan kan tsallako daga jihar Zamfara zuwa Kebbi domin su tada zaune tsaye a jihar ne sannan kafin mu kama su, sun riga sun kashe mutane biyar ranar 20 da 22 ga watan Afrilu sannan suka sace baburan hawa 15.”
” Mun kama su dauke da bindigogi biyar, cebur 4, adduna hudu da layuka da dama.”
A karshe Kabiru ya ce sun aika da jami’an tsaro zuwa wannan yankin sannan za su kuma hada kai da masu ruwa da tsaki a yankin don kawo karshen wannan aika-aika.”
Discussion about this post