Rahotanni sun tabbatar da tsaurara tsaro a garin Makurdi, babban birnin jihar Benue a yau Litinin saboda jiran isar Shugaba Muhammadu Buhari.
An ga dimbin jami’an tsaro a wurare daban-daban, a cikin garin yayin da wasu kuma ke sintiri kan titina a cikin motoci da tankokin yaki.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito cewa tsaro ya yi kamari sosai har da karnukan da ke jin warin mai laifi da kuma warin kayan laifi da kuma sojoji na shawagi a cikin hekikwafta a sararin sama.
A daya bangaren kuma ko’ina ka zagaya a garin sai karar jiniya ka ke ji wadda jami’an tsaro ke ta karakaina a cikin motocin.