Mata da ke shan miyagun kwayoyi a Jihar Kebbi ya yi matukar karuwa – NDLEA

0

Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa (NDLEA) reshen jihar Kebbi ta bayyana cewa wani abin tashin hankali da ban takaici shine yadda mata a jihar suke shan miyagun kwayoyi babu kakkautawa.

Hukumar tace yawan mata karuwa ya ke yi a kullum a jihar.

Shugaban hukumar Suleiman Jadi ya sanar da haka yayin da kungiyar ‘National Council of Women Societies (NCWS)’ ta ziyarce shi a ofishin sa sannan ya bayyana cewa abin ta yi matukar muni yanzu.

Ya kuma yi kira ga kungiyar da su hada hannu da hukumar don gani an kawar da wannan mummunar dabi’ar daga jihar baki daya.

Share.

game da Author