Kasar Amurka za ta tallafawa wasu kasashen Afrika da dala miliyan 533

0

Sakataren gwamnatin kasar Amurka Rex Tillerson ya bayyana cewa gwamnatin Amurka za ta tallafa wa wasu kasashen Afrika dake fama da rikici da dala miliyan 533.

Ya ce za a yi amfani da wadannan kudade ne wajen tallafa wa wadannan kasashen da abinci musamman a kasashen dake fama da yunwa sannan da inganta rayuwar mutanen ta.

Rex ya kara da cewa cikin kudin za a samar da dala miliyan 128 musamman domin Najeriya da kasashen dake kusa zagaye da tafkin Chadi.

Sauran kasashen da zasu amfana da wannan tallafi sun hada da Najeriya, Itofiya, Somaliya, Sudan ta Kudu da kasar Chadi.

Ana sa ran a ganawar Rex da shugaba Buhari, zasu tattauna ne kan yadda kasar Amurka zai ci gaba da taimaka wa Najeriya kan tsaro da sauran su.

Share.

game da Author