Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya ragargaji Ministan Lafiya, Osagie Ehanire da sauran manyan jami’an Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, saboda ƙaurace wa Taron Daƙile Korona da su ka yi.
Ehanire da Ƙaramin Ministan Lafiya Olorunnimbe Mamora da Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya duk ba su halarci taron ba.
Taron dai Kwamitin Daƙile Korona da kuma Majalisar Dattawa ne su ka shirya shi, domin tattauna hanyoyin daƙile korona da yadda za a farfaɗo da tattalin arziki.
Lawan ya ce ministocin biyu da sauran manyan jami’an ma’aikatar ilmi ba su kyauta wa kan su ba, kuma ba su kyauta wa ‘yan Najeriya ba.
“Kafin na fara jawabi, na duba amma ban ga Ministan Harkokin Lafiya shi da ƙaramin ministan lafiya ba da kuma Babban Sskatare na Ma’aikatar Lafiya. Gaskiya rashin zuwan na su ba daidai ba ne. Kuma ba su kyauta ba.
A makon jiya ne dama Majalisar Tarayya ta gargaɗi NCDC da Ma’aikatar Lafiya kada su yi wasa da rayukan jama’a.
Majalisar Tarayya ta gargaɗi Hukumar NCDC cewa ta tsaurara binciken-ƙwaƙwaf tare da ɗaukar matakai a kan masu shigowa cikin ƙasar nan.
Wannan gargaɗi ya zo ne a ranar Talata, ranar da NCDC ta bayyana ɓullar cutar korona nau’in ‘Omicron’, wadda aka samu ƙwayoyin cutar a jikin wasu matafiya biyu da su ka shigo daga Afrika ta Kudu.
Majalisar ta kuma yi kakkausan kira ga Mai’aikatar Harkokin Lafiya ta Tarayya cewa kada ta tsaya jan-ƙafa har cutar ta fara fantsama a cikin ƙasar nan.
Majalisar ta yi wannan kiran bayan amincewa da ba’asin da Ɗan Majalisar Tarayya Dachung Bagos (ɗan PDP daga Jihar Filato) ya yi a lokacin zaman majalisa, ranar Talata.
Baya ga Najeriya, wasu ƙasashen da cutar korona nau’in ‘Omicron ta ɓulla, sun haɗa da: Birtaniya, Belgium, Botswana, Jamus, Italiya, Hong Kong, Isra’ila, Jamhuriyyar Czech, Netherlands, Denmark da Austaraliya.
Tuni dai manyan ƙasashen duniya sun hana shiga ƙasar su daga ƙasashen Kudancin Afrika, waɗanda su ka haɗa da Afrika ta Kudu, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Nsmibiya da Zimbabwe.
A ranar Talata ce NCDC ta sanar cewa wasu matafiya biyu sun shigo da mummunar korona samfurin ‘Omicron’ cikin Najeriya.
Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta bayyana cewa cutar korona samfurin Omicron mai saurin maƙure mutum ta kashe, ta shigo Najeriya.
Cikin jawabin da Babban Daraktan NCDC, Ifedayo Adetifa ya fitar a ranar Talata da dare, ya ce an samu wasu matafiya mutum biyu da su ka shigo da cutar daga Afrika ta Kudu.
Ya ce an tabbatar da haka ɗin bayan wani gwaji da aka yi a Babban Ɗakin Gwajin Abuja.
Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki biyu bayan ƙasar Kanada ta bayyana cewa an matafiya biyu daga Najeriya ɗauke da cutar korona samfurin Omicron a Kanada.
A kan haka, NCDC ta ce ta ƙara miƙewa tsaye wajen tsaurara matakai.
Sannan kuma ta na ƙara kira da a gaggauta zuwa ana yin rigakafin korona.
Wannan jarida a ranar Talata ta buga labarin cewa Samfurin ‘Omicron’ mai saurin maƙure mutum ta kashe ba ta iso Najeriya ba.
Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta bayyana cewa sabuwar korona mai saurin maƙure mutum ta kashe farat ɗaya ba ta shigo Najeriya ba.
Sabuwar cutar ta korona samfurin Omicron (SARS-Cov-2) dai a yanzu ta tashi hankulan duniya, inda a na ta ɓangaren Najeriya ta haramta wa ‘yan ƙasar nan shiga ƙasahe irin su Afrika ta Kudu, Botswana, Italy, Jamus, Belgium da Birtaniya, inda cutar ta ɓulla.
Cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar raanr Asabar da dare, Darakta Janar na hukumar, Ifedayo Aderifa ya ce cibiyar NCDC na sa-ido tare da lura da halin sa ake ciki kada cutar ta shammaci ƙasar nan.
Ya ce kuma duk halin da NCDC ke ciki, za ta riƙa sanar da jama’a
Discussion about this post