Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana yadda tattaunawar sa da jigon APC, Bola Tinubu ta kasance a Lagos.
A ranar Lahadi ce Tinubu ya aika da jirgin musamman zuwa Abuja, aka ɗauki Shekarau zuwa Legas, inda su ka shafe sa’o’i uku su na tattauna matsalar APC a Kano.
Manyan biyu sun gana kwana biyu bayan Gwamna Ganduje ya je ya sanar da Tinubu musabbabin rikicin.
Shekarau ya shaida wa BBC Hausa cewa ya amsa kiran Tinubu a matsayin sa na uban jam’iyya, domin shi ma ya sanar da shi na sa ba’asin, tunda Ganduje ya je an ji ta bakin sa.
APC a Kano ta dare gida biyu, inda ɓangaren Ganduje da na Shekarau kowane ya yi zaɓen shugabannin jiha da na ƙananan hukumomi da mazaɓu daban-daban.
Bayan taron, Shekarau ya ce ya shaida wa Tinubu cewa ba Ganduje ba ne matsalar APC, amma matsalar ta shugabancin jam’iyya.
“Na shaida wa Tinubu cewa matsala ce ta shugabancin jam’iyya, saboda an ware ɓangaren mu, ba a yin komai da mu.
“Shi kuma Tinubu ya shaida min cewa Ganduje ya ce ya sanar da shi nasa bangaren. Shi ya sa ya gayyace ni, domin ni ma ya ji ta baki na.”
Premium Times Hausa ta buga Guduma 7 Da Kotu Ta Buga Bisa Kan Ganduje Cikin Watan Nuwamba.
A bisa dukkan alamu Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fara hango ƙarshen zangon mulkin sa na biyu, tun yanzu sama da shekara ɗaya kafin ya fita daga gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Ganduje wanda har yau fatalwar zaɓen ‘inkwankulusib’, wanda aka ce bai kammalu ba ba ta fice daga cikin ƙwanƙwaman kan sa ba, a ɗaya gefen kuma har yau akwai kurwar zargin cushe-cushen miliyoyin daloli a kan sa.
Waɗannan fatalwa da kurwa za su daɗe a jikin sa kafin ya samu makarun da zai karya su a fitar masa da su, bayan ya sauka daga mulki, cikin 2023.
Guduma 7 Kan Ganduje:
Cikin watan Nuwamba, Gwamna Abdullahi Ganduje ya biya tarar sa da kotu ta ci har naira 800,000 saboda ya ɓata wa Ja’afar Ja’afar suna.
Ja’afar shi ne ya fallasa zargin Ganduje da aka nuno shi ya na cusa daloli aljihu.
Wannan kuɗi dai tuni har Ja’afar ya ɗora naira 200,000 a kai, sun cika miliyan ɗaya, kuma ya ce a yi ayyukan taimakawa ga mabuƙata da kuɗin.
Guduma ta biyu a kan Ganduje ita ce soke zaɓen APC ɓangaren Abdullahi Abbas da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi a ranar 30 Ga Nuwamba.
Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya ce shugabannin APC ta ɓangaren tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ne halastattun shugabanni, a ƙarƙashin Haruna Ɗanzago.
Guduma ta uku da kotu ta ranƙwala wa Ganduje, ita ce umarnin da kotun ta bayar cewa kada ɓangaren Ganduje ya sake yin wani zaɓen shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ɗirka wa Ganduje kulki na huɗu, inda ta haramta korar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa Murabus Sarki Muhammadu Sanusi II.
Kotun ba ta tsaya nan ba sai da ta muƙa wa Ganduje kulki na biyar, inda ta ce ya biya Sanusi diyyar tauye masa ‘yanci har naira miliyan 10.
Guduma ta shida ita ce umarnin da kotun ta bayar cewa Sanusi na da ‘yancin dawowa Kano ya ci gaba da zaman sa. Ko kuma ya riƙa shigowa birnin a duk lokacin da ya ga dama.
Kotu ta ɗirka wa Ganduje guduma ta bakwai, inda ta umarce shi da ya buga roƙon neman afuwa ga Murabus Sarki Muhammadu Sanusi II a jaridu biyu na ƙasar nan.
Waɗannan batutuwa duk a cikin watan Nuwamba su ka faru, waɗanda ko shakka babu dukkan su babu wanda Ganduj cie zai yi farin ciki da shi. Domin tuni har ya fara gaganiyar tattara bayanan ɗaukaka ƙara.
Dama kuma wani sharhi da wannan jarida ta buga, ya yi tambaya shin Jagaban zai sasanta shi da Ganduje ne, ko saɓule wandon alaƙa zai yi daga ƙugun Gwamna ya ɗaura wa Malam?
A ranar Lahadi ce dai Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya yi wa Sanata Ibrahim Shekarau gayyatar gaggawa zuwa Legas daga Abuja.
Makusantan Shekarau sun tabbatar da cewa jirgi sukutum Jagaban ya tura Abuja aka ɗauki Sanata Shekarau zuwa Legas, inda ya shafe sa’o’i uku su na ganawa.
Hadiman na Shekarau sun ce daga cikin batutuwan da aka tattauna, har da sarambe da azargagin da Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi a wurin zaɓen shugabannin APC, wanda ya janyo har jam’iyyar ta dare biyu a Kano.
An kuma tattauna yadda su ka shigar da ƙara da yadda kotu ta halsata zaɓen da ɓangaren Shekarau su ka yi, inda su ka zaɓi Haruna Ɗanzago a matsayin shugaban jam’iyya a Kano.
Sannan kuma Shekarau ya yi masa bayanin yadda aka banka wa ofishin su wuta, kwana biyu bayan da kotu ta ba su nasara da kuma yadda gwamnatin Kano ta rufe ofishin lauyan ɓangaren Shekarau.
Idan ba a manta ba, Prmii Times Hausa ta buga labarin cewa ɓangaren Shekarau da Sanata Barau Jibrin sun kai koke wurin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya.
Discussion about this post