Jam’iyyar NNPP da wanda ya ƙirƙiro ita kan ta jam’iyyar, sun nuna mamaki dangane da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke na cire Gwamna Abba Yusuf daga gwamna.
Alƙalai uku ne dai suka yi zaman cire gwamnan tare da yanke hukuncin cewa shi ba mamba ba ne na NNPP a lokacin da aka yi zaɓen gwamnan Kano, wanda aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
Kotun dai ta ce Nasir Yusuf na APC ne ya yi nasara, kamar yadda Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen 2023 ta Kano ta yanke hukunci a cikin watan Oktoba.
Hashimu Ɗanguguwa, wanda su ne suka kafa NNPP, ya tattauna da manema labarai a Kano, inda ya ce hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke barazana ce ta ɗorewar dimokraɗiyya a Najeriya.
“Hukuncin barazana ce ga ɗorewar dimokraɗiyya a Najeriya z saboda al’umma sun zaɓi Abba a zaɓen da babu maguɗi a cikin sa.
“Saboda ba mu yi tsammanin haka Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yanke hukuncin ba.
“Amma idan aka dubi irin yadda kotuna ke yanke hukunci a yanzu, to lokacin wa’adin dimokraɗiyya ya gabato a Najeriya.
“Ban ga dalilin da zai sa mutum ya kewaya lungu da saƙon karkara ya yi takara, a zaɓe shi, sannan wasu mutum biyu ko uku su zauna kotu su tsige shi ba.”
A nasa ɓangaren, Gwamnan Kano ya bayyana cewa, ‘Zan ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli, domin a yi min adalci’.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya bayyana aniyar sa ta garzayawa Kotun Ƙoli, domin sake ƙalubalantar tsige shi da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe ta Abuja ta yi a ranar Juma’a.
“Ina sanar da al’ummar Jihar Kano da sauran ‘yan Najeriya cewa, bisa matsayar da masu ruwa da tsakin jam’iyyar mu suka cimma, mun umarci lauyoyin musu gaggauta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli.
“Mu na da yaƙinin cewa a Kotun Ƙoli a a yi mana adalci, ta hanyar jingine rashin adalcin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta yi mana a Kano.
“Muna kuma da yaƙinin cewa Kotun Ƙoli za ta tabbatar mana da zaɓen mu da al’ummar Jihar Kano su ka yi.” Haka gwamnan ya tabbatar, a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna ɗin, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar.
Yusuf ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar jihar Kano su ci gaba da gudanar da harkokin su, yayin da gwamnati ta ɗauki matakan da suka wajaba, domin tsare dukiyoyi da rayukan jama’a.
Ya tabbatar da cewa ɗan tsaikon da aka samu ba zai sare wa gwamnatin guiwa ba, wajen ci gaba da ƙoƙarin da ta ke yi domin gina ayyukan raya jiha da inganta rayuwar al’ummar jihar baki ɗaya.
Maimakon haka, Abba ya ce zai ci gaba da bijiro da ayyukan more mulkin dimokraɗiyya ga al’ummar jihar Kano.
Daga nan ya yi kira da ‘yan jiha da ƙasa baki ɗaya su ci gaba da yi wa Jihar Kano addu’a, domin Allah ya kuɓutar da ita daga rashin adalcin da aka yi wa jihar.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa Gwamna Abba bai cancanci zama gwamna ba, domin a cewar ta, a lokacin da aka yi zaɓe, shi ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne.
Kotun bisa jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, ta ce wasu adadin ƙuri’un da aka dangwala wa Abba a lokacin zaɓe, ba su da tambarin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), Olumide Akpata, ya ce duk inda ka ga an samu mai shari’a nagari a ƙasar nan, to dace ne kawai, amma shi ma ɗin ba ta hanyar da ta dace aka naɗa shi ba.
Akpata ya ce tsarin da ake bi ana naɗa masu shari’a a Najeriya, a lalace ya ke, dalili kenan martabar fannin shari’a ba shi da wata daraja yanzu a Najeriya.
Tsohon Shugaban na NBA, ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Ƙungiyar Lauyoyi na Duniya, a Paris, babban birnin Faransa.
Da ya ke jawabi a gaban mahalarta taron, Akpata ya ce matsayin Najeriya mai mafi yawan ɓaƙar fata a duniya, ƙasar na fama da wani “kamun-kazar-kuku” da gungun ‘yan siyasa suka yi wa fannin shari’a.
Ba shi kadai ya yi irin wannan kukan ba, shi ma farfesan shari’a, kuma tsohon Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam (NHRC), Chidi Odinkalu ya watsa wannan bayani a shafin sa na Tiwita a ranar Juma’a.
An nuno Akpata a cikin wasu gajerun faifan bidiyo biyu ya na nuna damuwa kan yadda masu mulki suka ƙudundune fannin shari’a, su ka cusa aljifan su.
Akpata wanda ta yi Shugaban NBA daga 2021 zuwa 2022, ya bayyana yadda tsarin naɗa alƙalai ya lalace a Najeriya.
“Inda duk ka ga an naɗa alƙali nagari, to sa’a ce kawai aka yi, amma ba bisa cancanta aka zaɓe shi ba. Saboda tsarin da ake bi ana naɗa alƙalai gurɓattacce ne.”
A matsayin Akpata lokacin da ya ke Shugaban NBA, ya na cikin Majalisar Kula da Alƙalai ta Ƙasa (NJC). Wannan majalisa ce ke naɗa masu shari’a a manyan kotunan Najeriya. Kuma ita ce ke ladaftar da alƙalan da aka kama da laifi.
“Lokacin da ina Shugaban NBA, na gano yadda masu mulki ke ƙudundune fannin shari’a, su na jefawa aljifan su. Hakan ya lalata tasirin tsarin shari’a sosai a ƙasar nan. Kuma su dai kam su na cin ƙazamar riba da irin wannan tsiyar da suke tsulawa.”
‘Alƙalan Ƙarambosuwa A Wasu Kotunan Najeriya’ – Akpata
“Wato wasu alƙalan da ake naɗawa wai masu shari’a, gaskiya magana wurin bai cancance su ba, kuma naɗa su zubar ƙimar fannin shari’a ne.”
Ko kwanan nan shi ma Odinkalu ya fito ya yi taratsi kan naɗa wasu alƙalai, irin su Babban Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola da Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara da sauran su.
Ya soki naɗe-naɗen da suka yi wa ‘ya’yan su da matan su a matsayin alƙalai. Da yawan ‘ya’yan wasu alƙalan da suka yi ritaya da waɗanda ke kan aiki, su ma an naɗa su alƙalai a ƙasar nan.
Akpata ya koka kan yadda gwamnoni ke yadda suka ga dama da alƙalan jihohi, ta hanyar hana su haƙƙin su da dakar ƙasa ta wajabta a yi masu.
Discussion about this post