Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu a hadarin jirgin ruwa da aka yi a karamar hukumar Shiroro dake Jihar Niger.
Shugaban fannin bada tallafi na hukumar bada agajin gaggawa na jihar NSEMA Garba Salihu ya sanar da haka ranar Juma’a a garin Minna.
Salihu ya ce hukumar ta samu labarin cewa jirgin ruwan da ya taso daga kauyen Zangoro Bassa/Kukoku za shi Gijiwa/Kato duk a karamar hukumar Shiroro ya yi hadari a ranar 6 ga Nuwamba da misalin karfe biyu na rana.
Ya ce jirgin ya yi hadari yayin da yake jigilan mutum 34 inda a ciki akwai maza 20 da mata 14.
Salihu ya ce an ceto mutum 24 sannan mutum 10 sun mutu.
“Wadanda suka mutu sun hada da Farida Muntari, Sharhabila Sagir, Abubakar Sadiq, Na’ima Ibrahim, Amina, Safaratu Ibrahim, Sadiq Ibrahim da Rafiya Yakubu.
Ya ce akwai mutum shida dake cikin jirgin da suka iya ruwa da suka hada da Dahiru Yusuf, Sa’idu Shu’aibu, Ahmadu Garba, Sa’idu Garba, Abdulaziz Yahaya da Lukuman Sani.
Salihu ya ce cikowar kogin sannan kuma jirgin ya yi karo da wani itace shine dalilin da ya sa ya kife a tsakiyar ruwa.
Ya ce jami’an karamar hukumar da jam’ian NSEMA sun fara gudanar da cigiyar sauran mutanen da suka bace a wannan kogi.
Discussion about this post