An yi karon-battar feshin ruwan bayanai tsakanin lauyan ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi da lauyoyin INEC, Tinubu da kuma na APC a ranar Talata.
A ranar ce dai aka kammala sauraren ba’asi daga ɓangaren mai ƙara, wato Peter Obi da kuma waɗanda ake ƙara, INEC, Shuhaban Ƙasa Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC.
Yayin da kotu ta bakin Shugaban Alƙalai biyar masu shari’ar, wato Haruna tsammani ya bayyana cewa nan gaba zai sanar da su ranar da za a yanke hukunci, waɗanda ake ƙara sun riƙa yi wa kotu bayani ɗaya bayan ɗaya su na roƙon a yi watsi da ƙarar da Peter Obi ya shigar.
Sun riƙa bin ƙorafe-ƙorafen da Obi ya yi na rashin sahihancin zaɓen Tinubu, su na karewa, domin ƙoƙarin gamsar da masu shari’ar su biyar.
Ɓangarorin uku sun yi wa Obi rubdugun cewa ya kasa kawo hujjoji a dukkan bayanan rashin cancantar Tinubu da ya ke ta hayagaga a kai.
Misali, lauyan Tinubu Wole Olanipekun, ya ce batun zargin an taɓa kama Tinubu da ƙwaya a Amirka har aka ƙwace dala 460,000 a hannun sa, wannan ai Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya wanke Tinubu tun tuni.
Sai dai kuma lauyan Peter Obi ya ce ɓangarorin na INEC, Tinubu da APC duk borin kunya su ke yi, sun kasa kare waɗanda ya ke ƙara.
Ya ce ya na da yaƙinin hujjojin da ya gabatar sahihai ne, kuma kotu za ta yi la’akari da su.
Haka kuma a ranar an gwabza tsakanin lauyan Atiku Abubakar da lauyoyin INEC, APC da Tinubu.
Kuma a dai ranar ce sairaren shari’a tsakanin Atiku da Tinubu ta ƙare, saura bayyana ranar yanke hukunci kaɗai ya rage.
Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Shugaban ta bayyana cewa nan gaba za ta bayyana ranar da za ta yanke hukuncin ƙarar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ya kai Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen, Haruna Tsammani ne ya bayyana hakan a ranar Talata, cewa za a sanar wa ɓangarorin biyu ranar da za a yanke hukuncin.
Atiku ya maka Tinubu, APC da INEC kotu, inda ya ƙalubalaci nasarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.
A zaman kotun na ranar Talata, lauyan INEC Abubakar Mahmoud ya roƙi kotu ta yi watsi da ƙarar da Atikun ya shigar, domin a cewar sa, babu wasu hujjojin da shi Atiku ɗin ya bayar.
Lauyan INEC ya ce an samu nasara wajen amfani da na’urorin BVAS da IReV a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya ce “‘yar matsalar da ta faru yayin loda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, tsawon sa’o’i huɗu da minti 50 kacal.”
Haka kuma ya ce tattara sakamakon zaɓe da aka yi da hannu ba da na’ura a wasu wurare, ai bai dagula sakamakon zaɓen ba.
Shi ma lauyan Tinubu wato Wole Olanipekun, cewa ya yi tattare sakamakon zaɓen ba da na’ura ba, bai rage masa sahihanci ba.
Ita ma APC ta roƙi kotu ta yi fatali da roƙon da Atiku ya yi mata, domin ya kasa gabatar da hujjoji da zai tabbatar da shi ne ya yi nasara, da kuma maguɗin da ya ke cewa an yi masa.
Tunda an kammala sauraren ɓangarori, za a yanke hukunci kafin ranar 16 Satumba.
Discussion about this post