An bayyana cewa duk tsananin talaucin da ke damun masara galihu, matsawar ba ka da asusun ajiya a banki, to ba ka da rabo a cikin tallafin.
Wale Edun ne ya bayyana haka, a lokacin da Majalisar Dattawa ke tantance shi, a matsayin Minista, a ranar Talata.
Ya ce za a yi amfani da hanyoyin tantance marasa galihu ne ta bayanan zamani da su ka haɗa BVN da lambar asusun ajiyar kuɗaɗe a banki.
Edun wanda ya na cikin waɗanda aka tantance a ranar Talata, ya fito ne daga Jihar Ogun.
Ya ce haka za a bi a tantance dukkan marasa galihu miliyan 12 da za su ci gajiyar tallafin na Naira miliyan 8,000.
Ya yi bayanin ne a matsayin amsar da ya bai wa Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.
Lawan ya tambayi Edun cewa idan har ya kasance shi aka naɗa Ministan Harkokin Kuɗaɗe, shin ta yaya tallafin Naira 8,000 zai isa ga marasa galihun da ko asusun ajiyar kuɗaɗe a banki ba su da shi.
Edun ya amsa masa da cewa, idan shi ya zama Ministan Harkokin Kuɗaɗe, to “komai talaucin mutum ba zai samu ba, sai fa idan ya na da asusun ajiyar kuɗaɗe a banki.”
Har ma ya kafa misali da ƙasar Indiya, wadda ta umarci kowane gida ya buɗe asusun ajiyar kuɗaɗe na ‘yan gidan bai-ɗaya.
Tuni dai ‘yan Najeriya su ka raina wannan tallafi na Naira 8,000 da za a raba wa mutum miliyan 12, a lokacin da za a yi wa ‘yan majalisa watandar Naira biliyan 110.
Discussion about this post