Siyasar 2023 zai sauya zani matuka ba kamar yadda wasu ke tunanin jam’iyya mai mulki ita ce za ta yi nasara a jihohi da kujerar shugaban kasa ba.
Jihohin Kaduna, Katsina da Kano, sune ake yi wa kirarin 3k saboda ruwar kuri’u da sukan yi wa ‘yan takara a zabe. Duk dan takarar da ya samu wadannan jihohi musamman a zaben shugaban kasa, to lallai akwai yiwuwar zai yi nasara a zabe, musamman na shugaban Kasa.
Toh sai dai kuma wannan karon kila ba a zaben shugaban kasa ne za a sami matsala ba, tun a zaben gwamnoni da na yan majalisu za a samu matsalar gaske.
Sanata Uba Sani shine ake sa ran zai gaji gwamna mai ci Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Nasiru Gawuna kuma zai gaji Abdullahi
Ganduje na jihar Kano sai kuma Dikko Radda wanda zai gaji Aminu Masari na jihar Katsina a jam’iyyar APC dukkan su.
Bisa ga yanayin da siyasa ta karkata a yanzu, akwai alamun talakawa sun ja bakin su ne sun yi shiru tsit, suna jiran a fito filin daga su nuna karfin su da kuri’un su.
Jihar Kaduna
Jihar Kaduna da ake mata kirari da cibiyar Arewa ba a barta a baya ba. Har yanzu akwai alamun akwai lauje fa a cikin nadi, domin duk da zabin Uba Sani a matsayin dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, wasu da dama a cikin jigajigan jam’iyyar sun ja bikin su ne sun yi shiru kawai amma ba haka aka so ba.
Masu yin sharhi na ganin har yanzu kakakin majalisar Jihar Kaduna, Yusuf Zailani bai yi na’am ba da zabin sanata Uba Sani. Sai dai kuma bisa ga abinda ake gani a fili, an yi sulhu kuma tafiyar daya ce. Kakakin majalisar jihar, Zailani yana bangaren tsohon kwamishinan kasafin kudin Jihar ne, Muhammed Sani Dattijo wanda shine yanzu dan takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya.
Honarabul Isah Ashiru ne dan takarar kujerar gwamna na jihar Kaduna PDP. A hira da yayi da PREMIUM TIMES HAUSA, Ashiru ya ce wannan karon shine zai yi nasara a zaben gwamna na jihar Kaduna. Babban dalilin sa kuwa ita ce wai mutane sun dandana salon APC sun ji a jika.
Jihar Katsina
A jihar Katsina ma abin ya fi muni, domin baya ga shugaban Kasa da ya zama dan asalin jihar, jihar na daga cikin jihohin Arewa da matsalar rashin tsaro yayi tsananin gaske. Sannan kuma hatta wasu daga cikin makusantan shugaba Muhammadu Buhari da suka hada da sanatan da ke wakiltar shiyyar sa da dan uwansa dake wakiltar Daura duk sun fice daga APC.
Abubuwa ya dagule matuka a jihar, kowa ya harzuka sannan kuma shi kansa zabin gwamna Masari wato Radda, ba shine mutane hatta yan jam’iyyar ke so ba kamar yadda wasu suka shaida wa PREMIUM TIMES Hausa.
A jam’iyyar PDP , akwai Lado Dan Marke wanda shine dan takarar gwamna a jihar. Ga dukkan alamu mutanen Katsina ba su ji dadin mulkin APC ba kuma suna jiran su a filin daga. Akwai yiwuwar wannan karon dai PDP ce za yi nasara a zaben gwamnan na jihar Katsina, sai dai kuma babbar katangar da ke a tsakaninta da gidan gwamnati shine, shugaban kasa dan jihar Katsina ne sannan kuma gwamna shi kansa dan jam’iyyar APC ne.
Jihar Kano
Jihar Kano dai kaifi daya ce, Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP. Kalubalen da ke gabar NNPP ita ce yadda za ta fafata da Gawuna na jam’iyyar APC. Sannan kuma akwai Mohammed Abacha na PDP duk da cewa akwai rikici a ciki har yanzu.
Ficewar Shekarau jam’iyyar NNPP ya dada dagulawa jam’iyyar NNPP lissafi sai dai kuma wasu na ganin Shekarau ya fice a kurarren lokaci, domin duk wata jam’iyya da zai koma ba zata yi masa tasiri ba sannan shima ba zai yi mata tasiri ba a zabe mai zuwa.
Discussion about this post