IƘIRARI: Kwanan nan aka yaɗa wani hoto da aka nuna “shafin farko” ne na jaridar PUNCH a soshiyal midiya inda aka nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe zunzurutun kuɗi har naira biliyan 5 da miliyan ɗari tara (N5.9bn) wajen horas da matasa guda 177 kan yadda ake gyaran wayar hannu.
CIKAKKEN LABARIN: A wannan “shafin farkon” da aka yaɗa, an rubuta ɓaro-ɓaro cewa, “Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kashe naira biliyan 5.9 wajen horas da matasa 177 kan gyaran wayar hannu,” labarin da ya jawo maganganu da suka mai yawan gaske daga ‘yan Nijeriya.
Wani mai amfani da Instagram ya yi tsokaci a kan zancen inda ya ce, “Don Allah ko akwai wanda zai ba ni ruwan sha kofi ɗaya, Nijeriya ta kusa sanya ni in suma! Ban da dukkan rancen kuɗin da ake karɓowa, in ba a ce dabbobi ba, ɓeraye da ƙwari sai kuma a ce … wai har yanzu biliyan na da ziro guda tara ne? Akwai buƙatar mu #sakekarɓarnaija #tsaftacenaija #sakeginanaija.”
Wani kuma ya hau Tuwita ya yi tsokaci kamar haka: “Do Allah, ko akwai gwanayen lissafi a nan? Don Allah ku lissafa, ina so in ga nawa ne ake nufin APC ta kashe a kan waɗannan matasan bogin su 177?
“Ya ku Matasa, kafin ku goyi bayan haukan nan da ake kira APC, ku tuna da wannan kanun labarin. In da an yi amfani da wannan kuɗin ta hanyar da ta dace, ai da mun samu matasa masu amfanarwa.”
TABBACI: Jaridar PRNigeria ta lura da cewa wannan hoton ya na da tambarin ‘watermark’ “- 6mdh – photogrid” wanda ya sa ake ganin sa kamar tambarin jaridar PUNCH na gaske ne aka ɗauko daga masu amfani da soshiyal midiya daban-daban, saboda haka sai mu ka yi amfani da hikimar bincike ta ‘reverse image search’ a manhajar Google, a ƙarshe sai sakamakon ya nuna mana cewa hoton wanda ya yi kama da na bangon gaba na mujalla babu inda ya fito a cikin shafukan zahiri na jaridar PUNCH da ke soshiyal midiya, kawai wasu masu amfani da shafukan zumunta ne su ka riƙa tura shi nan da can a Tuwita da Instagram.
Daga nan jaridar PRNigeria ta tuntuɓi sashen yaɗa labarai na Ma’aikatar Harkokin Jinƙai domin tabbatar da gaskiyar wannan magana, to amma sai wani jami’i da ya roƙi mu sakaya sunan sa ya bayyana lamarin da “Labarin bogi.”
Sai dai da PRNigeria ta gudanar da bincike kan wasu muhimman kalmomi a wurare daban-daban, ta gano cewa duk da yake hoton da aka yaɗa ƙarya ne, shi labarin ba ƙarya ba ne amma kuma rahoto ne da ya fito watanni huɗu da su ka gabata.
Gaskiya ne cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana a cikin Afrilu 2022 cewa ta ware kuɗi naira biliyan N5.9 domin horaswa da samar da kayan aiki da biyan alawus-alawus a kowane wata kan Rukunin C na shirin ‘N-Power’ a Jihar Kano, ba wai a kan matasa 177 kacal ba. Gwamnatin ta nanata cewa kimanin matasa 16,629 ne su ke amfana da shirin (ƙarƙashin Rukunin C) a jihar, ta ƙara da cewa a ƙiyasi har mutum 18,042 sun ci moriyar shirin a Rukunin A da na B na shirin.
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ita ce ta ba da wannan bayanin ta hannun Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman a Koyar da Sana’o’i, Dakta Nasir Mahmoud, lokacin da ya wakilce ta a wajen bikin yaye ɗaliban shirin ‘N-Skills’, wanda wani sashe ne na ‘N-Power’, wanda aka yi a Kano, inda aka horas da matasa 177 kan gyaran waya.
Wannan bayanin ne jaridar PUNCH ta ɗauka ta lauya shi ta buga labarin da ya yaudari masu karatu, wanda tuni ta gyara labarin.
KAMMALAWA: Bisa ga shaidar da jaridar PRNigeria ta harhaɗa, mun gano cewa iƙirarin wai Gwamnatin Tarayya ta kashe naira biliyan 5.9 kan horas da matasa guda 177 su iya gyaran waya ba gaskiya ba ne. An fara buga rahoton a cikin jaridar PUNCH (shi ma ba a shafin farko ba) wanda tuni sun gyara shi tunda matasa 177 ɗin da ake magana wani sashe ne kaɗai daga cikin jimillar matasa 16,629 da za a horas a Rukunin C na shirin ‘N-Power’ a Jihar Kano waɗanda za su amfana da naira biliyan 5.9 da Gwamnatin Tarayya ta kasafta. Haka kuma, hoton da ake yaɗawa ba daga ita kan ta jaridar PUNCH ya fito ba, kawai wasu ne su ka ƙirƙire shi domin su yaudari jama’a.
Discussion about this post