Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan da wani soja ya yi wa Sheikh Goni Aisami a Jihar Yobe.
Soja John Gabriel ya bindige Aisami bayan ya ɗauke shi a motar sa ya rage masa hanya, daga Nguru kafin a ƙarasa Jaji-Maji a Ƙaramar Hukumar Karasuwa.
“Wannan kisan dabbanci ne ƙarara. Ta yaya sojan da aka yi wa horo da bin ƙa’idar kare rayukan jama’a, amma ya kashe mutumin da ya ji tausayin sa ya rage masa hanya a motar sa?”
“A matsayi na na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, na yi baƙin ciki da kuma harzuƙa da wannan mummunan kisa, wanda babban laifi ne a ce jami’in tsaron da aka yi wa horon kare rayukan jama’a ya aikata.”
“Bisa irin horon soja da aka yi mana, an yi mana kakkausan hani ga aikata irin wannan mummunan laifi. Ba ɗabi’ar sojojin ƙwarai ba ne su cutar da mutanen da ba su aikata laifin komai ba.
“Wannan laifi da sojan ya aikata, ba halayyar sojojin mu ba ce, amma kuma za ta iya shafa wa sauran sojoji kashin-kaji, ta kankare masu kima a idon farar hula.”
“Wannan mummunan al’amari zai iya sa ‘yan Najeriya su fara jin tsoron bayar da taimakon jinƙai ga sojojin mu. Kuma hakan zai iya rusa kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin sojojin Najeriya da farar hula.
“Ina kira ga mahukuntan sojojin Najeriya su ladabtar da duk wani mai hannu a cikin wannan mummunar aika-aikar, ba tare da ɓata lokaci ba. Kuma a bankaɗo duk wasu irin wannan munanar ɗabi’a.” Inji Buhari.
Buhari ya yi ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Yobe, al’ummar jihar da kuma iyalan mamacin.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga ba bayanin Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Yobe, inda ya ce tun da farko dama da shirin tare motoci ya yi fashi da makami soja Gabriel ya fita kafin ya bindige Sheikh Aisami.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta tabbatar tare da bayyana yadda Lance Kofur John Gabriel ya kashe Sheikh Goni Aisami a Jihar Yobe.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce Gabriel wanda yanzu haka yake hannun su shi da wani sojan da ya yi ƙoƙarin taya shi tserewa da motar malamin, dama can a wannan daren da abin ya faru, ya yi niyyar fita ya tare motoci ne domin ya yi fashi da makami.
“John Gabriel da Adamu Gideon duk su na aiki ne a Bataliya ta 241 da ke Nguru. Gabriel shi ne soja mai lamba NA/13/69/1522, shi kuma Gideon NA/13/70/6552.
“Gabriel ya fito daga barikin sojan Nguru ne da niyyar tafiya fashi da makami ta hanyar tare motocin matafiya. Ya fito ya tsaya a shingen sojoji ɗauke da ɗan gadon kambed, wanda ba a sani ba ashe ya naɗe bindiga ya ɓoye a cikin gadon.
“Ya tsaye sai ga Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a mota ƙirar Honda mai lamba KBT 31 AE, inda Gabriel ya tsayar da shi, ya ce ya rage masa hanya.
“Su na tafiya an kai wajen Jaji-Maji cikin Ƙaramar Hukumar Karasuwa, sai soja Gabriel ya ce Malam ya tsaya, kamar ɗaya tayar gaba ta na ƙara.
“Ko da Malam ya fita domin ya duba taya, sai Gabriel ya ɗirka masa bindiga, sannan ya ja gawar sa, ya kai ta can cikin daji.”
Abdulkarim ya ƙara da cewa soja Gabriel ya kira abokin sa soja Adamu Gideon domin ya taimaka masa, bayan ya kasa guduwa da motar malamin, saboda ta ƙi tashi.
Ya ce wani mai wucewa zuwa gona ne ya ga gawar malamin a daji da kuma mota, ya garzaya ya sanar wa ‘yan sandan Jaji-Maji, waɗanda su ka duƙufa aikin su, har su ka kamo sojojin biyu.
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda sun samu bindigar sojan da kuma wata mota ƙirar Sharon a wurin da aka yi kisan.
“Tuni dai wanda ya yi kisan ya amsa laifin sa.” Inji Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim.
PREMIUM TIMES dama ta buga labarin cewa soja Gabriel tsohon ɓarawo ne, ya taɓa yi wa Kwamandan Bataliyar Sojojin 241 da ke Nguru satar naira 480,000, har kwamandan ya tsine masa, kuma ya ce da yardar Allah Gabriel ba zai yi kyakkyawan ƙarshe ba.
Discussion about this post