YUNWA: Adesina da mashahuran masana 24 na duniya sun roki Amurka ta taimaka a kauce wa barkewar yunwa a duniya

0

Shugaban Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, Akinwumi Adesina da wasu gaggan masana ilmin kimiyya da masana tattalinarziki da mashahuran masu bncike 24 na duniya, sun rubuta wa Shugaban Amurka Joe Biden wasikar neman rokon Amurka ta yi amfani da karfin arzikin ta a kawar da yunwa a duniya, nan da shekarar 2030.

Masanan sun ce ya dace matuka Amurka ta shiga sahun kasashen dunya domin a kawar da yunwa ta hanyar kafa gagarimar cibiya idan an je Taron Majalisar Dinkin Duniya kan Abinci.

“Yayin da duniya ke tafiya da kyar tun bayan dukan tsiya da barkewar cutar korona ta yi, to tun daga wannan shekara ta 2021 ya kamata a fara gagarimin shirin kawar da yunwa a duniya, nan da shekarar 2030.

“Yunwa ta fi yi wa milyoyin mutane barazanar kisa a duniya fiye da cutar korona. Domin idan jikin mutum babu abinci, to magani ma ba zai yi amfani ko tasiri a jikin ba. Abinci da kayan sinadaran gina jiki sun a rigakafin yunwa. Ya kamata mu yi wa duniya rigakafin yunwa.” Inji Adesina.

Farkon wannan makon ne PREMUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa yunwa ta darkako Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20.

A ckin labarin, Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi gargadin cewa yunwa ta darkako Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20 daban-daban na duniya.

Wasu kasashen da hukumar ta FAO ta yi gargadin cewa yunwa ta nausa kuma ta darkaka sun hada da Afghanistan, Yemen, Congo, Sudan, Habasha, Haiti da Syria.

Wadannan kasashe 20 da hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta lissafa, ta ce nan da ’yan watanni za su iya fadawa cikin halin matsananciyar yunwa, idan ba a gaggauta yin wani kokarin cetar da yankunan ba.

Rahoton wanda na hadin-guiwa ne tsakanin FAO da Cibyar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ya kuma yi nuni da cewa

nan da watan Yuli wadannan kasashe za su shiga matsanancin karancin abinci, don haka akwai bukatar samar da tallafin gaggawa a wuraren da ake ganin matsalar za ta fi shafa matuka.

Rahoton ya danganta kazamin rikicin da ake yi tsakanin Yemen da Saudiyya ne zai jefa wani yanki na kasar Yemen cikin matsanciyar yunwa da karancin abinci.

“Sama da mutum miliyan 16 a kasar Yemen ka iya fuskantar matsanciyar yunwa da karancin abinci musamman zuwa cikin watan Yuni, 2021.

A Arewacin Najeriya kuwa, rahoton ya ce ana tsoron karancin abinci tsakanin watannin Yuni, Yuli da Agusta, sakamakon rikice-rikicen ’yan bindiga da Boko Haram a Arewacin Najeriya.

Rahoton y ace matsalar da aka fuskanta a shekarar da ta gabata, za ta iya nunkawa a wannan shekara.

“Nan da watanni shida akalla mutm miliyan 13 za su iya afkawa cikin gagarimar matsalar karancin abinci da matsananciyar yunwa a Arewacin Najeriya.” Haka dai rahoton ya tabbatar.

Dama kuma kusan mutum milyan 32 na rayuwar ‘ya-mu-samu-ya-mu-sa-bakin-mu’, kamar yadda rahoton ya jaddada.

A cikin rahoton, Babban Daraktan Abinci na Hukumar FAO, QU Dongyu ya bayyana cewa matsalar da ta tunkari wadannan kasashe abin tayar da hankali ce matuka.

“Ya zama wajinin mu a tashi a gaggauta yanzu-yanzu domin hakan zai iya cetar rayuka dama, kuma za a hana barkewar mummunar matsala.” Gargadin Dongyu kenan.

Share.

game da Author