Buhari ya kaddamar da Shirin Noma da Girbin Shinkafa a Arewa-maso-Gabas

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana nasarar noman shinkafar da aka samu na daya daga cikin nasarorin gwamnatin sa, tare kuma da irin gagarimin tsayin-dakan da cibiyoyin da ke kula da shirye-shiryen, irin su Babban Bankin Najeriya (CBN).

Buhari ya yi wannan jawabi ga taron bukin kaddamar da noman shinkafa a Arewa-maso-Gabas, shiri na 202i, tare da kaddamar da girbi da kuma sayar da samfarerar shinkafa ga masu masana’antun casar shinkafa a Jihar Gombe.

Buhari wanda Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya wakilta a wurin bukin, ya nuna godiya ga irin kokarin da bankin CBN ya yi wajen warware matsalar noman shinkafa, ta hanyar samar da kudade ga manonan shinkafar a kasar nan.

Sannan kuma ya gode wa gwamnoni da su ka shiga gaba wajen kokarin ganin shirin bunkasa noman shinkafa ya bunkasa a kasar nan.

Buhari ya jinjina wa Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe saboda kokarin da ya yi wajen farfado da noman auduga, wanda Gombe ta yi suna a fannin, tsawon shekaru masu yawa a baya.

Shugaban Kasa din ya ce duk da irin karancin kudin da gwamnatin sa ke fama da kuma fuskanta, hakan bai hana gwamnatin samun gagarimar nasara wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan ba.

A nasa jawabin, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ba don Shugaba Buhari ya bijiro da shirin bunkasa noma ba ta hannun Babban Bankn Najeriya (CBN), to irin tulin dalar buhunnan shinkafar da ake kallo a wurin taron sai dai a gani mafarki kadai.

Share.

game da Author