Nusaiba Shuaibu-Ahmad ƴar asalin jihar Kano ta lashe gasar musabaƙar karatun alkur’ani a ɓangaren izu 60 mata da aka kammala yau asabar a jihar Kano.
An fara musabakar ne kwanaki takwas baya, a cikin Jami’ar Bayero dake a birnin Kano.
Muhammad Auwal, daga Jihar Zamfara shi ne gwarzon musabakar na bana a bangaren Maza
Gwarzayen sun kara da masu karatu da yawa in da a karshe suka yi nasara a matakin karatun izufi 60 da tafsiri.
Malama Nusaiba daga bangaren mata, wadda ita ma ta zo ta daya a bangaren izufi 60, kuma yar asalin jihar Kano ce.
A yayin bikin, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya nadawa Muhammad Auwal rawani, cewa ya zama kangaran kuma zakaran gwajin dafi a tsakanin gwanayen masu karatun al-Kur’ani mai girma.
Zakarun sun samu kyautar Naira miliyan biyu da rabi ko wannansu.
Hamshakim dan kasuwa, Aminu Alhassan Dantata ya bayar da kyautar miliyan goma ga kwamitin shirya gasar Alkur’ani mai girma ta kasa.
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III ya halarci wurin rufe wannan gasa ta karatun al-Kurani.
Discussion about this post