Buhari ya sha aradun sauko da tsadar farashin kayan abinci

0

A karkashin wannan alwashin sauko da tsadar farashin kayan abinci, Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi Babban Bankin Najeriya kada ya kuskura ya bada canjin dala ga duk wanda zai yi odar kayan abinci daga waje.

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki a yarda da alwashin da ya sha cewa gwamnatin sa za ta sa ido sosai a kan tsadar kayan abinci a cikin shekarar 2021.

A kan hakan ne Buhari ya gargadi Babban Bankin Najeriya kada ya kuskura ya bada canjin dala ga duk wanda zai yi odar kayan abinci daga waje.

Da ya ke jawabi a wurin taron su na Majalisar Mashawartan Shugaban Kasa kan Harkokin Tattalin Arziki, Buhari ya ce “Jihohi bakwai na kasar nan su na noma dukkan shinkafar da ake bukata a ci a kasar nan. Don haka tilas mu hakura mu ci abincin da mu ke nomawa.”

Ya ci gaba da bayanin irin bunkasar da harkokin noma ya samu a kasar nan daga dogaron da ake yi kan fetur, Buhari ya ce a wannan kokari da gwamnatin sa ta yi, ya ce ba don cutar korona ta kawo wa Najeriya cikas ba, da ba a san irin bunkasar da kasar za ta yi a duniya ba a fannin noma.

“A lokaci daya kuma farashin yadda ake biyan kudin lebura kafin a hako ganga daya, ya karu ainun, idan aka yi la’akari da arhar aikin leburancin hako danyen man fetur a kasashen Larabawa.” Inji Buhari.

Ya yarda cewa dole sai an bai wa harkar noma muhimmanci, amma kuma a lokaci guda, tilas sai an dakile matsalar tsadar kayan abincin da ake nomawa a cikin kasa.

“Mu dai za mu ci gaba da kara wa jama’a kwarin guiwar cewa a tashi a koma gona. Saboda masu hannu da shuni da rikakkun ‘yan boko sun nuna mana cewa wai arziki na wajen danyen mai. Su ka sa aka yi watsi da harkar noma. Yanzu ya ku ke tsammani idan da ba mu rufe kan iyakokin mu ba, kuma ba mu zaburar da jama’a sun koma gona ba. Ai da yanzu mu na cikin wahala tantagaryar ta.” Inji Buhari.

Share.

game da Author