Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi Allah-wadai da kashe-kashen rayuka da lalata dukiyoyi da aka yi a kudancin Jihar Borno da kuma Jihar Adamawa.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakatare na ma’aikatar, Bashir Nura Alkali, ya rattaba wa hannu, an ruwaito cewar ministar ta girgiza matuƙa da labarin da ta ji na hare-haren ta’addancin da aka kai a ƙauyen Pemi da ke Ƙaramar Hukumar Chibok da wasu ƙauyuka huɗu da ke Ƙaramar Hukumar Hawul a kudancin Borno da kuma garin Garkida da ke Jihar Adamawa.
Ta bayyana hare-haren da sunan marasa tausayi kuma na rashin imani.
Ta ce, “A gaskiya abin baƙin ciki ne a ce an yi waɗannan hare-haren ta’addancin a daidai lokacin da ya kamata a ce mutane su na jin daɗin hutun Kirsimeti tare da masoyan su.
Ta ce, “Ina miƙa jaje na ga gwamnati da jama’ar Jihar Borno musamman iyalan waɗanda wannan abin baƙin cikin ya shafa.”
Ministar ta nanata cewar Gwamnatin Tarayya ta yi tir da hare-haren, kuma ta jinjina wa hukumomi daban-daban da kuma Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ba tare da ɓata lokaci ba ya kai ziyara a ƙauyukan da abin ya shafa tare da bada umarnin a tsaurara matakan tsaro a yankunan.
Hajiya Sadiya ta bayyana cewar ana nan ana shirye-shirye domin a kai kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa don a rage masu raɗaɗin hare-haren da aka kai masu.
Rahotanni dai sun bayyana cewa a ranar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020, wato ana gobe Kirsimeti, ‘yan Boko Haram sun kai hari a garin Garkida da ke Jihar Adamawa inda su ka kashe mutum biyar sannan su ka banka wa motoci da gidaje wuta, su ka ƙone su.
A Pemi da ke Jihar Borno ma, a wannan ranar, ‘yan ta’addar sun kashe mutum biyar tare da lalata majami’u da makarantu da gidaje.
Shugabannin siyasa na yankin tare da sauran masu sa ido sun yi tir da hare-haren.
Discussion about this post