ZABEN EDO: APC ta taya Obaseki murna, ta ce nasarar sa nasarar dimokradiyya ce

0

Shan dukan tsiya da jam’iyyar APC ta yi a zaben Gwamnan Jihar Edo, bai hana ta aika sakon taya murna da fatan alheri ga Gwamna Godwin Obaseki ba, wanda ya lashe zaben a karkashin jam’iyyar PDP.

Shugaban Riko na APC na Kasa, kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, yadda aka gudanar da zaben a cikin ruwan sanyi da kuma nasarar dimokradiyya ce a Najeriya.

Buni ya yi wannan bayani cikin wata takarda da ya fitar a ranar Litinin a Damaturu, inda ya kara da cewa APC da Shugaba Muhammadu Buhari za su ci gaba da gudanar da zaben da babu katsalandan ko magudi a cikin sa.

Ya ce wannan abub ne mai matukar muhimmanci domin kara karfafa tiraku da ginshikin tafiyar da mulki a kasar nan.

Buni ya fitar da wannan bayani, lokuta kadan bayan da Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya isa Abuja ya gana da Buhari, bayan dawowar sa daga zaben Jihar Edo.

Jami’ai dai ba su bayyana abubuwan da Buhari ya tattauna shi da Ganduje ba. Amma dai ana ganin ba zai rasa nasaba da zaben Edo ba, wanda APC ta yi rashin nasara.

Sai dai kuma duk da APC ta Kasa ta taya murna ga PDP ko kuma dan takarar ta Gwamna Obaseki, dan takarar APC, Ize-Iyamu ya ce an yi masa magudi. Kuma ya na shawarar mataki na gaba.

Haka kuma APCin Jihar Ekiti ta zargi Gwamnan Ekiti da goyon bayan Obaseki na PDP a zaben Edo.

Wasu mambobin jam’iyyar APC reshen Jihar Ekiti, sun zargi Gwamna Kayode Fayemi na jihar da goyon bayan Godwin Obaseki na Jihar Edo, a zaben gwamna, wanda Obaseki din ya kayar da Ize-Iyamu na APC.

Gwamnan Ekiti dai dan APC ne, kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.

Wadanda su ka zarge shi din sun ce a yanzu haka ya na kitsa tuggun da zai sa ya kore su daga jam’iyyar baki daya.

Tsawon watanni da dama kenan rikici ya tirnike jam’iyyar APC a Jihar Ekiti.

Cikin makon da ya gabata, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa an gayyaci Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Siyasa, Babafemi Ujudu, shi da wasu cewa su bayyana gaban kwamiti domin amsa tamboyoyin dalilin rashin bin umarnin jam’iyya da su ka yi.

An nemi a ji dalilin da ya sa su ka ki janye kararrakin da su ka maka APC a gaban alkalan kotuna badan-daban.

A martanin su wanda su ka turo wa PREMIUM TIMES, sun ce babu wata jam’iyya da ta gayyace su, Gwamna Fayemi ne dai kawai kanwa-uwar-gamin gayyatar su din da aka yi.

Share.

game da Author