ZABEN EDO: Mun garkame zakuna da damisa cikin keji a gidan ‘zoo’ – Gwamna Obaseki

0

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki, ya bayyana cewa sake zaben sa karo na biyu ta nuna cewa sun garkame zakuna da damisar da su ka addabi siyasar jihar baki daya.

Ya ce a yanzu dai duk wata karya da fankama ta kare, sun garkame duk wata damisa da zakunan siyasar Edo a cikin keji, a gidan zoo.

Obaseki ya yi wadannan kalaman a dandazon taron ‘yan PDP a dandalin Kings Square a ranar Litinin a Benin, babban birnin Jihar Edo, bayan kammala zagayen nuna godiya ga dimbin magoya bayan sa da su ka zabe shi karo na biyu.

Daga cikin ‘yan tawagar gwamnan akwai Mataimakin sa Philip Shaibu, Shugaban Kamfen din Gwamna, Dan Orbih, mamba na Majalisar Tarayya, Ogbeide Ihama da sauran su.

Obaseki ya kara da cewa sakon da jama’a su ka aika a lokacin zaben da aka gudanar ranar Asabar, “ya nuna na je na yi wa al’ummar Jihar Edo aiki tukuru. Wato tabbas al’ummar jihar Edo sun fito sun yi magana da babbar murya, yadda kowa da kowa ya saurare su.”

“Kun taimaka min na damke zakuna da damisar da su ka yi gangami a Edo ranar zabe. Na kulle su a gidan ‘zoo’, a cikin keji. Ba ku kara ganin su a Edo, saboda su na can a kulle cikin keji. Dama can din ne ya cancanci wurin zaman da ya dace da su.” Inji Obaseki.

“A yau ina yi ma ku alawarin cewa za mu yi wa Jihar Edo aiki sosai, saboda wani gogarman da zai rika yi masa katsalandan, ko kawo mana cikas a kokarin samar wa ‘yan Jihar Edo kayan inganta rayuwa.

“Ni da mataimaki na Philip Shaibu za mu koma ofis mu ci gaba da yi wa jama’a aiki.”

A karshe ya gode wa daukacin jama’a baki daya.

Share.

game da Author