Manoman albasa na bukatar karin kudade wajen habbaka noman albasa

0

Sakataren Kungiyar Masu Noman Albasa ta Najeriya, Aliyu Umar, ya yi kira da a kara damfara jari da makudan kudade wajen noman albasa, domin kara bunkasa noman ta da cin moriyar albarkatun da ke tattare da noman na albasa.

Umar ya yi wannan kira a lokacin da ya ke magana wurin taron dashen irin albasa, a kauyen Tunga da ke cikin Kasamar Hukumar Raba a Jihar Sokoto, a ranar Talata.

Ya bayar da shawara cewa Najeriya ta kara maida hankali wajen noma, domin gaggauta farfado da tattalin arzikin kasa.

Sakataren kungiyar ta manoman albasa, ya jinjina wa gwamnatin tarayya a kan kokarin ta da jajircewa wajen ganin ta tayar da komadar tattalin arzikin kasa ta hanyar noma. Musamman ya yi magana a kan Shirin Bayar da Lamuni ga Manoma daga CBN, wato ‘Anchor Borrower Scheme.’

Ya ce irin wadannan tallafin ramcen kudaden noma da ake bayarwa, sun taimaka wajen bunkasa noman albasa, inda ya tashi daga noman a sayar da albasa a sayi abinci zuwa noma na bunkasa arziki.”I na so ku sani cewa akwai albarkatu dankam a harkokin noman albasa.

“A Jihar Sokoto aka fi noma albasa a kasar nan. Tsakanin Afrilu zuwa Agusta an sayar da albasa za ta kai ta naira milyan hudu.

“Ko barkewar cutar Korona da kuma ambaliyar da ake fama da ita, wadanda su ka kawo tsaiko da gurgunta harkoki, mu dai ba su hana mu noma da hada-hadar albasa ba.” Inji.

Babban Jami’in Harkokin Noma na Babban Bankin Najeriya, CBN, da ke Reshen Sokoto, Abdullahi Farouk, ya bayyana cewa dama shi Shirin Ramcen Noma na CBN, wato Anchor Borrower Scheme, an kirkiro shi ne domin bunkasa bangarori daban-daban na harkokin noma.

Share.

game da Author