Dalilin da ya sa na dakatar da Magu, muka sa a bincike shi – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wasu dalilan da ya sa ya rattaba hannu don dakatar da shugaban hukumar EFCC, na riko Ibrahim Magu.

A takarda ta musamman wadda kakakin fadar gwamnatin Buhari, Garba Shehu ya fitar a madadin Shugaba Buhari ya ce Magu bai fi karfin a bincike shi ba duk da shine shugaban hukumar dake bankado barayin gwamnati.

” An mika mana tulin takardun korafe-korafe game da irin harkallar da Magu ya aikata. Da yawa daga ciki ana zargin sa da yin sama da fadi da kudade da wasu da bai dace ba ace a matsayin sa na shugaban hukumar EFCC ya cusa kan sa a ciki ba.

” A dalilin haka muka ga ya da ce lallai a gudanar da bincike akan wannan hukuma, shugabanta da wasu manyan jami’an hukumar. Wannan shine ya sa tunda abin ya kai ga haka dole sai an dakatar da shi da wadanda ake zargi sun dulmiya kansu a harkallar handame kudaden da ake zargin sun bace a hukumar.

” Abinda ya fi dacewa shine ya sauka daga kujerar shugabancin hukumar domin a samu damar iya gudanar da bincike yadda ya kamata. Barin su akai zai iya kawo wa masu bincike cikas a aikin su.

” Wadanda suke ganin binciken Magu da ake yi yanzu kamar yaba wa kasar nan kashi ne a fuska, toh lallai kam an tafi an bar su, domin basu yi kyakkyawar nazari ba.

” Abinda ake yi wa Magu yanzu shine ya fi dacewa a yi domin nuna wa duniya cewa lallai Najeriya da gaske ta ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa da ta sa a gaba, tunda dai gashi ma wanda aka dora ya jagoranci hukumar na fuskantar binciken harkallar kudade a kasar.

” Magu bai fi karfin gwamnati ba, ganin irin abin kunyar da yake neman jefa wannan gwamnati a ciki a matsayin sa na shugaban hukuma irin ta EFCC.

Share.

game da Author