Sallamar matasan dake cikin Shirin N-Power babu tallafi Itama wata Annobar ce, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Shirin Npower yazo ne a karkashin alkawarin aikin yi da gwamnatin APC tayi wa matasan Najeriya lokacin kamfen din neman kuri’arsu. Hakan ne yasa matasa suka fito kwansu da kwarkwatarsu wajen jefawa jam’iyar kuri’a a ranar zabe. Jefa kuri’a a lokacin ya zamo wa matasan tamkar gwagwarmayar neman tsira.

Sabanin wancan alkawari na bayar da aiki ga miliyoyin matasa a kowacce shekara da gwamnatin tayi. A shekarar 2016 ne aka fara gudanar da tsarin Npower a matsayin aikin wucin-gadi na shekara 2 ga matasan. Shirin ya fara ne da matasa dubu dari biyu (200,000) da farko. Sannan daga baya aka sake daukar guda dubu dari uku (300,000). Wanda a cikin 2017 ya bayar da mutum dubu dari biyar (500,000) suna kar6ar dubu talatin wata (30k) duk wata.

Rukuni na farko (Batch A) na shirin sun samu wata Arba’in da daya (41 months) suna cin moriyar tsarin yanzu. A yayin da rukuni na biyu (Batch B) zasu cika shekara biyu dindi a karshen watan nan (July). Rukuni na farko an basu babbar waya (Device) kirar “tablet” wacce wasunsu da yawa sun fara kasuwanci da ita. A yayin da rukuni na biyu ba a basu ba.

Akwai bambanci na wata goma sha bakwai (17 months) a tsakanin rukuni na farko da rukuni na biyu. Wanda zai baiwa ‘yan rukuni na farko samun kudi Naira miliyan daya da Dubu Dari Biyu da Talatin (1,230,000). Su kuma ‘yan rukuni na biyu zasu samu kudi a cikin shekara biyu har Naira Dubu Dari Bakwai Da Ashirin (720,000). Tsakanin ‘yan rukuni na farko da na biyu akwai akalla bambancin Naira Dubu Dari Biyar Da Goma (510,000).

Bayan dauke shirin daga ofis din mataimakin shugaban kasa zuwa sabon ministry a karkashin sabuwar minista Sadiya Umar Farouk sai abubuwa suka canza. Abu na farko shine barazanar kora da rashin biya akan lokaci. A karshe dai cikin tsakiyar annobar coronavirus aka fitar da lokacin sallamar wadannan matasa gabadayansu.

Abun tambaya a nan shine:

1 – Ina maganar baiwa matasa aikin yi a lokacin kamfen?

2 – Ina maganar kudin sallama da minista ta rika yin alkawari a hira daban daban?

3 – Ina wayoyin ‘yan rukuni na biyu? Ya za a yi da maganar bambancin wa’adi tsakanin rukunin farko da na biyu?

4 – Shin ana zaton annobar coronavirus bata shafi “saving” din wadannan matasan ba?

5 – Waye zai ciyar da iyalan masu aure a cikinsu? Ko yin aure ga matashi dan shekara 35 haramin ne?

Allah ya kiyaye

Share.

game da Author