Komawar Aminu Babba Dan Agundi Cikin Masarautar Kano, Kashi na 2, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabinmu Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa baki dayansu. Bayan haka:

Ya ku al’ummah, lallai addinin mu na Musulunci addini ne da ya umurci mabiyansa da su kasance akan dabi’u da halaye na gari, har ta kai sai da Manzon rahama, Annabi Muhammad (SAW) yayi nuni da cewa an sanya manufar aiko shi ya zamanto domin ya cika kyawawan halaye da dabi’u masu kyau. Yana mai cewa:

“An aiko ni ne kawai domin in cika kyawawan halaye da dabi’u na gari.”

Kuma lokacin da Allah yayi nufin yayi yabo ga Masoyinsa Annabi Muhammad (SAW), ya yabe shi ne da kyawawan halaye da dabi’u na gari. Yana mai cewa:

“Lallai kai ma’abucin halaye ne madaukaka.”

Kuma yayin da yayi nufin ya tunatar da al’ummah game da rahamar da yayi masu, na aiko Annabi Muhammad (SAW), yayi nuni ne da taushin halinsa, yana mai cewa:

“Saboda rahama daga Allah ne kake tausaya masu.”

Ya ku jama’ah, akwai nassoshi masu yawa da suka zo suna nuna muna muhimmancin kyawawan halaye da dabi’u na gari, har Al-Kur’ani mai girma ya kasance idan ya ambaci wasu ukubobi yakan raba su da ambaton afuwa da yafiya, wadanda suke wani bangare ne daga cikin kyawawan halaye da dabi’u na gari, kuma ya ambaci afuwa da cewa tafi kusa da tsoron Allah.

Bayin Allah masu girma, daga cikin kyawawan halaye da dabi’u na gari, akwai FADIN GASKIYA, da tsayawa akan gaskiya, da kasancewa tare da masu gaskiya, da taimakon gaskiya a duk hali da yanayi da mutum ya samu kan sa a ciki. Allah Ta’ala yana cewa:

“Ya ku wadanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah, ku kasance tare da masu gaskiya.” [Suratut-Taubah: 119]

Kuma Allah Ta’ala yace:

“Ya ku wadanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah, kuma ku fadi magana madaidaiciya.” [Suratul-Ahzab: 70]

Ya ku bayin Allah, a wadannan ayoyi na Alkur’ani mai girma, Allah ya umurci bayin sa muminai da su kasance tare da masu gaskiya, kuma su kasance masu fadar magana madaidaiciya, wato ta gaskiya, wadda ta ke kan hanya. Saboda haka ya zama dole, ya zama wajibi, ya zama tilas ga mutumin kirki, a duk inda yake, ya goyi bayan gaskiya da masu gaskiya, ba tare da tsoron kowa ko shakkar wani ba. Idan kuwa mutum yaki goyon bayan gaskiya da masu gaskiya, saboda son zuciya ko saboda kwadayin wani abun duniya, ko saboda kusancinsa da mutum, to ya sani, lallai Allah zai kama shi, zai azabtar da shi, kuma mun san kamun Allah ba sauki ne da shi ba!

Ya ku jama’ah, lallai ku sani, hakika shi goyon bayan gaskiya da masu gaskiya da tsayawa akan gaskiya da fadin gaskiya da aikata gaskiya cikin mu’amala da magana da sauran al’amurran rayuwa ibadah ne, kuma cikar kamala ne, nagarta ne, kuma riko ne da addini, sannan yana daga cikin kyawawan halaye da dabi’u na gari, domin yin hakan umurni ne daga Allah, Mahaliccin mu.

Sannan kuma duk mutumin da ya riki gaskiya to da wuya ace yau gaskiyar sa ta kare, domin Allah Ta’ala yana tare da masu gaskiya, kuma yayi alkawarin kasancewa tare da su a koda yaushe, zai taimake su, kuma zai ci gaba da dora su akan makiyansu!

Sannan lallai duk wanda ya dage wurin jiyar da al’ummah gaskiya komai dacinta, to lallai za su godewa dandanon zakin yin hakan a karshe, ko da ya hadu da wahalhalu a farkon al’amari.

Hakika a duk inda ka samu mai fadin gaskiya tsakaninsa da Allah, da jajircewa, da tsayawa akan maganarsa, zaka samu wasu mutane da basa son gaskiyar sun sa shi a gaba da zagi, tsangwama, batanci, la’anta, cin mutunci, da kokarin ganin bayansa da kokarin tozarta shi. Amma a daya gefen kuma, zaka samu rayuwarsa ta zama da ban sha’awa, ga kuma samun sauki da taimakon Allah, kuma zai samu shaida mai kyau ta yabo daga mutanen kirki, nagartattu.

Wasu mutane da basu fahimci al’amurra ba suna ta mamakin yadda muka tsaya tsayin daka muna kare Sarki Muhammadu Sanusi, muna goyon bayan sa, kuma muna kokarin kare masa mutuncin sa da martabar sa. Wasu suna ganin ai wasu ke sa mu, ko wasu muke yiwa aiki. A’a, wallahi ko daya babu, kawai mu muna yin wannan ne saboda gaskiyar sa. Kuma ko ba Sarki Muhammadu Sanusi ba, mu a wurin mu, goyon bayan mai gaskya da kare shi ibadah ne kuma addini ne.

Saboda haka mu muna da yakini, a bisa iya binciken da muka yi, da kuma abunda Allah Ta’ala ya fahimtar da mu, cewa, a cikin dukkanin wannan badakala, Sarki Sanusi aka zalunta, kuma shi aka danne wa hakki, shi yasa muke ta kokarin kare masa mutuncinsa da martabar sa. Kuma wallahi mun dauki yin hakan a matsayin ibadah, kuma a matsayin addini. Sannan a iya binciken mu game da waye Sarki Sanusi? Meye dabi’un sa da halayen sa? Allah ya fahimtar da mu cewa shi mutumin kirki ne. Sannan duk abun da makiyansa da masu yi masa hassada suke yi na kokarin bata masa suna, da yi masa sharri da kazafi, duk karya ne ba gaskiya ba ne.

Allah Ta’ala, ta harshen Manzon sa, Annabi Muhammad (SAW), ya tilastawa Musulmi cewa dole ne su tsaya tsayin daka, su canza, kuma su dakatar da barna da rashin gaskiyar da yake gudana a tsakanin su. Idan kuma sun ki yin hakan saboda wasu dalilai na son zuciyar su, to lallai akwai matsala. Ina rokon Allah ya kare mu, amin. Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Duk wanda ya ga abun ki, marar kyau, na rashin gaskiya, a tsakanin ku, ko a cikin ku, to ya canza shi da hannun sa. Idan ba zai iya canza shi da hannun sa ba, to ya canza shi da harshen sa, idan ba zai iya canza shi da harshen sa ba, to ya ki abun a cikin zuciyar sa, kuma wannan shine mafi raunin imani.” [Muslim ne ya ruwaito shi, daga Hadisin Abi Sa’id Al-Khudri (RA)]

Sannan Annabi Muhammad (SAW) ya wajabta muna taimakon wanda aka zalunta, wato mu kwato masa hakkin sa, sannan kuma mu taimaki azzalumi, wato mu hana shi aikata zalunci. Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Ku taimaki azzalumi da wanda aka zalunta. Sai sahabbai suka ce ya Annabin Allah, mun san yadda za mu taimaki wanda aka zalunta, wato mu kwato masa hakkin sa. To shi azzalumi ta yaya zamu taimake shi? Sai Annabi Muhammad (SAW) yace, ku hana shi aikata zakuncin, shine kun taimake shi.”

Ya ku ‘yan uwa na masu daraja, idan baku manta ba kun san a cikin satin nan, nayi rubutu mai taken, ‘Abun Al’ajabi, Dawowar Aminu Babba Dan Agundi Cikin Masarautar Kano’, nayi bayani akan hakikanin gaskiyar abun da ya faru na cire rawanin Aminu Babba Dan Agundi, wanda baban mu, mai daraja, wato marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero (Allah ya haskaka kabarinsa) yayi, har zuwa mayar da shi kan sarautar sa da aka yi a yau? Kuma alhamdulillahi, wannan rubutu ya samu karbuwa sosai ta yadda ma ban yi tsammani ba. Miliyoyan mutane sun karanta, wasu sun kira mu, wasu sun aiko da sakon fatan alkhairi da jinjinawa, tare da addu’a da kara karfafa mani gwiwa. Ina godiya matuka zuwa ga ‘yan uwa na Kanawa da dukkanin ‘yan arewa da suka yaba da wannan rubutu da ya fayyace masu gaskiyar da suka dade suna nema. Dukkanin su ina mika sakon godiya ta a gare su, saboda kauna da soyayyar da suka nuna mani, tare da addu’ar Allah ya saka masu da mafificin alkhairi duniya da lahira, kuma ya bar zumunci, amin. Kuma In Shaa Allahu ina mai sanar da su cewa, ba zamu yi kasa a gwiwa ba wurin wayar masu da kai, tare da tsage gaskiya komai dacinta.

To bayan wannan rubutu nawa, da Allah ya albarkace shi, ya yadu sosai kamar wutar daji, sai wasu makiya gaskiya, masu adawa da ita hankalin su ya tashi, suka rude, suka rikice, suka dimauce, suka harzuka, suka yi fushi, ran su ya baci! Suka fara tunanin cewa yaya zasu yi su dauki mataki, ko su mayar da martani, ko su kare kan su akan wannan rubutu nawa. Sun nemi wasu ‘yan jaridu, marubuta, suka nuna masu cewa, wai zasu dauke su aiki domin suyi mani martani, zasu biya su. Wadannan ‘yan jaridu suka fada masu cewa, wannan bawan Allah fa gaskiya ya fada, kuma mu ba zamu yi masa martani akan gaskiyar da ya fada domin ya wayar da kan jama’ah ba. Wasu daga cikin wadannan ‘yan jaridu wallahi, Allah shine shaida, sun kira ni, kuma sun shaida man duk yadda aka yi.

Wani mutum ma, daga cikin masu fada da gaskiyar, wai shi mai ba wa gwamnatin jihar Kano shawara, kira na yayi, ya boye lambar sa, ya zazzagi iyaye na, yaci mutunci na, yace wai ina jawo masu bakin jini wurin al’ummah. Ni kuma na fada masa cewa, ni buri na shine in bayyana wa al’ummah gaskiya. Kawai nayi dariya, nace wannan ai matsoraci ne, domin idan ba tsoro ba, meye na boye lambar sa?

To babban dalilin da yasa nayi wannan rubutu da kuke karatu yanzu shine, saboda wani mutum da ya kira ni, yace shi yana cikin iyalin Babba Dan Agundi ne. Wannan mutum da jin muryar sa ba karamin yaro ba ne wallahi, babban mutum ne, kuma mai shekaru. Yayi man zagi na fitar hankali, ya ci mutunci na, ya zagi iyaye na, yayi zagin rashin mutunci, irin na maguzawa, tare da ashar da tsinuwa da la’ana da batanci iri-iri. Kuma wannan mutum ma daga karshe yace sai yasa an kashe ni, sai ya zama sanadiyyar bari na wannan duniyar, sai yasa an halaka ni. Ga lambar wayar sa nan zan rubuta domin duniya ta gani. Kuma wannan mutum ya manta da cewa yanzu muna cikin zamanin ilimin kimiya da fasaha ne, wanda gano ko waye shi ba zai zama wata wahala a gare mu ba? Ga lambar wayar sa kamar haka: 08035868648.

Wannan mutum, yayi man sharri, yayi man karya, kuma yayi man kazafi, yace wai wani ne yake daukar nauyi na ina yin rubutun da nike yi. Shine nayi dariya, nace wannan mutum wallahi bai san da wanda yake magana ba, shi yasa yake fadar wannan kazamar magana, yana dangantata zuwa ga re ni. Wallahi da ya san ni da bai fadi haka ba.

Abun da nike so duk wadannan mutane masu fada da gaskiya su sani shine, ita fa gaskiya idan Allah ya bayyana ta wallahi babu wani mahaluki da zai iya toshe ta. Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi alkawari sai ya bayyana gaskiya, saboda kowa ya gane ta, ya san ta, ya fahimce ta. Allah Ta’ala yace:

“Kuma kamar haka ne muke bayyana ayoyi, muke bayyana gaskiya dalla-dalla, domin hanya da tafarkin masu laifi ya bayyana (ya fito fili karara).” [Suratul An’am: 55]

Anan, Allah ne da kan sa yayi alkawarin tona asirin marasa gaskiya a duk inda suke, kuma ko su waye su!

Sannan Allah Ta’ala ya fada muna cewa, lallai zai yi amfani da gaskiya, da masu gaskiya domin ya yaki marasa gaskiya da mabarnata a cikin al’ummah a ko da yaushe. Allah Ta’ala yace:

“Muna jefa gaskiya akan karya, sai ta darkake ta, sai ta kasance halakakkiya. Kuma banin azaba ya tabbata a gare ku saboda abun da kuke siffantawa.” [Suratul Anbiya’: 18]

Kuma Allah ya fada muna cewa yana yin haka ne saboda ya banbance tsakanin karya da gaskiya, sai al’ummah su fahimci gaskiyar su bi ta, kuma su fahimci karya su guje mata. Allah Ta’ala yace yana yin haka ne domin:

“Ya rarrabe mummuna daga kyakkyawa, kuma ya tattara mummunan wuri guda (wani akan wani), sannan ya tura su gaba daya cikin wutar jahannama. Wadannan sune masu hasara.” [Suratul Anfal: 37]

Kuma Allah Ta’ala ya haramta muna goyon bayan marasa gaskiya ta ko wane hali. Saboda haka idan mutum ba ya da gaskiya, ko dan uwan ka ne, ko abokin ka ne, ko mai gidan ka ne, ko shugaban ka ne, kai ko iyayen ka ne, to haramun ne ka goyi bayan su. Haka kuma mai gaskiya dole ka goyi bayan sa, kuma ko da baka hada komai da shi ba. Idan kuwa ka bijire wa umurnin Allah, ka goyi bayan marasa gaskiya, saboda kusancin ka da su, to idan Allah zai yi masu azaba, zai hada da kai ne. Allah Ta’ala yace:

“Kar ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci (ku goyi bayan marasa gaskiya), sai (azabar) wuta ta shafe ku…” [Suratul Hud: 113]

Saboda haka sakon da nike isar wa zuwa ga duk wani makaryaci, mai barazanar banza, ya sani wallahi, wallahi, wallahi, babu abun da zai iya yi, domin ni ina tare da kariyar Allah ne a duk inda nike. Kuma ni ban tsoron kowa in ba Allah da ya halicce ni ba. Sannan kuma yin rubutu da fadin gaskiya komai dacinta, kuma ko akan waye, yanzu muka fara, kuma har zuwa lokacin da Allah ya dauki ran mu da ikon Allah. Kuma mu so muke yi Allah Ta’ala ya dauki ran mu akan wannan hanyar ta wayar da kan al’ummah, da bayyana masu gaskiya. Don haka su sani, babu-gudu-babu-ja-da-baya!

Yau shekara ashirin da biyar kenan ina yin wannan rubuce-rubuce, kuma alhamdulillah, Allah yana kare ni. Masu yin barazana da shirme irin wannan sun yi sun gaji sun kyale ni, wasunsu ma sun mutu, amma ni ga shi har yanzu Allah ya bar ni da rayuwata ina ta yi. Allah Ta’ala yace:

“Ka ce, Babu abun da zai same mu sai abun da Allah ya rubuta a gare mu. Allah shine majibincin mu. Kuma ga Allah kawai, sai muminai su dogara.” [Suratut-Taubah: 51]

Don haka wallahi babu abun da zai same ni sai abun da Allah Ta’ala ya kaddara zai same ni. Don haka duk wata barazana da wani zagi, da wani cin mutunci, wannan duk shirme ne wallahi. Kuma ni na san duk wanda ya zagi iyaye na, wallahi iyayen sa ya zaga, kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya tabbatar muna.

Kuma ni ina sane cewa, wannan shine tafarkin masu tsaya wa akan gaskiya. Don haka duk wani matsoraci, wanda bai shirya ya jurewa zage-zage da kazafe-kazafe da cin mutunci ko batanci akan fadin gaskiya ba, to don Allah ya sani, abun da yafi masa shine, ya koma gida yayi baccinsa. Idan yana da mata tayi masa fiffita, idan kuma ba ya da ita to yayi da kan sa. Domin ya sani, samun yarda da amincewar gaba dayan mutane, wani matsayi ne da ba mai iya riskar sa.

Rubutun da nike yi domin kare martaba da mutuncin Sarki Sanusi, da duk rubutun da nike yi domin tona asirin makiyansa, da wannan rubutu da nayi akan mayar da Aminu Babba Dan Agundi cikin masarautar Kano, bayan mai daraja, marigayi Sarki Ado Bayero ya tube masa rawani, duk rubutu ne da aka yi tsakani da Allah, kuma rubutu ne na gaskiya. Ba na yiwa kowa karya da sharri, kamar yadda su suke yi muna, amma da ikon Allah, zan fadi gaskiya, kuma wallahi komai dacinta! Don haka sai dai kuyi hakuri makiya. Idan ba ku so mu rubuta, to ku tsaya akan gaskiya, kar ku zalunci kowa, kuma ku bai wa kowa hakkinsa.

Wallahi su har kullun, mutane ne da ba za su iya zama haka nan, ba tare da sun yada karya akan Sarki Sanusi ba. Yanzu don Allah dubi irin karyar da suke yada wa a soshiyal midiya (social media), wai Aminu Ado ya nada Sanusi Lamido Sanusi sarautar Wamban Kano. Wace irin karya ce wannan? Wane irin munafunci ne wannan don Allah? Kuma a haka, wai suna so muyi shiru, kar mu fadi gaskiya! Haba wa!! Su ma sun san sam ba zai yiwu ba!!!

Allah ya jikan Malam Sa’adu Zungur, ya fada a cikin wasu baitoci nasa da suka shahara, yace:

“In zaka fadi, fadi gaskiya,
Komai taka ja maka ka biya!”

Shi kuma Imam Ahmad Ibn Hanbal Allah ya jikan sa da rahama, yace:

“Idan kai kayi shiru ka kame bakin ka daga fadin gaskiya, ni ma nayi shiru na kame baki na daga fadin gaskiya, kowa yayi shiru ya kame bakin sa daga fadin gaskiya, to ta yaya za’a yi wadanda basu san gaskiyar ba su fahimce ta, sannan kuma ta yaya za’a yi a karantar da al’ummah, kuma a wayar masu da kai?”

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurtamu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka a koda yaushe.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah, Muhammad (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, kuma ya kawo muna mafita ta alkhairi a cikin dukkanin al’amurran mu, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author