KIRAN TARON APC: Buhari bai karya dokar jam’iyya ba – Gwamna Bagudu

0

Gwamnan Jihar Kebbi kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya wanke Shugaba Muhammadu Buhari daga zargin cewa ya karya dokar jam’iyya da ya kira taron uwar jam’iyya a Zauren Taron Majalisar Zartaswa ta Fadar Shugaban Kasa.

Ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke komawa Birnin Kebbi, babban Birnin Kebbi.

A ranar Alhamis ce Buhari ya kira taron uwar jam’iyya a Zauren Majalisar Kasa, a inda shi ne Shugaban Kasa na farko da ya taba yin haka.

Bagudu ya ce dokar Najeriya ba ta haramta yin taron siyasa a Zaurwn Majalisar Fadar Aso Villa.

“Doka ya ce zai kasance Shugaban Kasa na cikin Majalisar Zartaswa na jam’iyya. Shi kuma jama’a ne suka hadu su ka zabe shi.”

Saboda haka sai Bagudu ya ce don Buhari ya kira taron ‘yan jam’iyya a zauren bai karya dokar kasa ba, ko kadan.

Ya ce Buhari mutum ne mai farin jinin da idan da ko shi kadai ya tsaya takarar zabe, zai iya ci ya yi nasara”.

Ya ce bai ga inda wani sashe na dokokin Najeriya ya hana yin taron masu ruwa da tsakin jam’iyya ba a Zauren Majalisar Taro na Shugaban Kasa.

Batun maganganun ko ya dace Ministan Shari’a Abubakar Makami ya rantsar da Shugaban Riko na APC, Bagudu ya ce babu wata matsala, Makami ya yi daidai.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga rahoton yadda Buhari ya kafa tarihin gudanar da taron jam’iyya a Zauren Majalisar Fadar Shugaban Kasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa tarihin zama shugaba na farko da ya shirya taron siyasa a Zauren Taron Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

A ranar Alhamis ce Buhari ya shirya taron na Majalisar Zartaswar APC, zauren da gwamnatin Najeriya ta kebe musamman saboda tarukan da suka jibinci sha’anin mulki da gudanarwar gwamnati.

Tsohon Shugaban Mulkin Soja Ibrahim Babangida ne ya gina zauren Majalisar cikin shekarun 1990, a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke kira Aso Rock.

A cikin wannan katafariyar majalisa ce shugabannin da suka gabata, suka rika shirts taruka da ministoci da kuma Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa da Majalisar Kolin Tsaro ta Kasa.

Dukkan wadannan taruka duk sha’anin mulki ne da gudanarwar al’amuran gwamnati ake shiryawa, ba taron siyasa ba.

Kuma a ciki ne wasu shugabannin ke karbar bakuncin masu kawo musu ziyara.

Duk da cewa babu wata dokar da ta hana gudanar da taron siyasa a cikin Zauren Fadar Shugaban Kasa, wannan dai ne karo na farko da aka taba shirya irin wannan taron, tun cikin shekaru 30 da gina majalisar.

Wannan ne kuma karo na farko da shirya irin wannan taron siyasa tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a cikin 1999.

A lokacin mulkin PDP, tun daga kan Olusegun Obasanjo har zuwa Umaru Yar’Adua da Goodluck Jonathan, a hedikawatar PDP suke gudanar da irin wannan taron.

Ita ma APC din tun bayan hawa mulkin Buhari a 2015, a hedikwatar jam’iyyar da ke Wuse 2 ta ke shirya irin wannan taron. Sai a wannan lokacin ne aka yi taron a Fadar Shugaban Kasa.

Shugaba marigayi ‘Yar’Aduwa ya taba shirya taron masu ruwa da tsakin PDP a ‘Yar’Adua Centre, Abuja.

Ba a dai san dalilin shirya taron a Zauren Majalisar Fadar Shugaban Kasa ba.

Sai dai kuma idan za a iya tunawa, kafin shirya taron, ‘yan sanda sun kewaye hedikwatar APC, sakamakon rikicin da ya rirnike jam’iyyar.

PREMIUM TIMES ta buga rahoton yadda Buhari ya karya dokar jam’iyyar APC, ya nada gwamnoni cikin Shugabannin Kwamitin Riko

Nadin da aka yi wa wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC cikin Kwamitin Shugabannin Riko, ya karya dokar jam’iyyar APC, kamar yadda PREMIUM TIMES ta bincika kuma ta bayyana.

A ranar Alhamis ne Babban Kwamitin NEC na zartaswa na APC ya rushe kwamitin Gudanarwa na NWC tare da nada mambobin kwamitin riko su 13, cikin su kuwa har da gwamnoni uku.

An dora musu nauyin rikon ragamar jam’iyyar har tsawon watanni shida nan gaba.

A taron da uwar jam’iyyar ta yi a Fadar Shugaban Kasa, an dora wa sabbin Shugabannin Riko su tabbatar sun shirya taron gangamin jam’iyya a cikin wadannan watanni shida, domin a zabi cikakkun shugabannin jam’iyya.

An kuma umarci mambobin APC kowa ya janye duk wata kara da korafe-korafen da aka kai juna a kotu.

Sun kuma amince da zaben da aka yi wa Osagie Ize-Iyamu a matsayin dan takarar APC a zaben jihar Edo, wanda za a yi a ranar 19 Ga Satumba.

Cikin wadanda suka halarci taron har Buhari, Mataimakin sa Yemi Osinbajo da kuma gwamnonin APC na kasar nan.

Gwamnoni uku da aka nada cikin shugabancin kwamitin su na Yobe, Mai-Mala Buni, wanda kuma shi aka nada Shugaban Riko na Kasa, sai Isiaka Oyetola na Osun da kuma Sani Bello na Neja.

Antoni Janar kuma Ministan Harkokin Shari’a na Kasa, Abubakar Malami ne ya rantsar da Gwamna Buni a matsayin Shugaban Riko.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta binciko cewa Kwamitin Zartaswar APC ya karya Sashen Dokar APC na 17 (v) na 2014 da aka yi wa kwaskwarima a cikin shekarar 2014 din.

Ga Abin Da Dokar Ta Ce:

“APC ba ta yarda kuma ba ta amince mutum ya kasance ya na rike da mukamin shugabanci a jam’iyya, kuma ya na rike da mukami a cikin gwamnati ba.”

Wannan sashe na doka kenan ya haramta gwamnonin uku zama shugabannin rikon jam’iyyar APC kenan.

Wani lauya mai suna Ken Asogwa, ya bayyana rashin jin dadin yadda APC ta karya dokar da ta gindaya da kan ta, duk kuwa da cewa a baya Kotun Koli ta gargadi jam’iyyun siyasa su daina karya dokokin da suka rattaba a cikin jam’iyyun su, domin rage yawan kararraki a gaba.

Sauran masana da lauyo yin da suka zanta da PREMIUM TIMES, duk sun nuna mamakin irin yadda APC ta tafka wannan gagarimin kuskuren da ake ganin zai rike mata wuya a gaba, har ta yi da-na-sani.

Tuni dai har bangaren NWC da aka tsige aka nada wasu, sun yi barazanar garzayawa kotu.

Masu hangen nesa na ganin cewa duk wani zabe da APC za ta shiga a karkashin wadannan Shugabannin Riko, zai zama haramtacce kenan.

Wato ko da ta yi nasara a zabukan gwamnan Edo da Ondo, kotu za ta iya kwacewa ta bai wa jam’iyyar da ta yi ta biyu.

Share.

game da Author