Gwamnan Ondo ya kamu da cutar Korona

0

Gwamnan Jihar Ondo ya shiga sahun jerin gwamnonin Najeriya da suka kamu da cutar Coronavirus.

A ranar Talata din nan ce Akeredolu ya sanar a shafin sa ta Tiwita cewa ya na barar addu’a, domin ya kamu da cutar Korona.

“An yi min gwaji, kuma an tabbatar ina dauke da cutar Coronavirus.

“Duk da cewa dai ba na jin wata alamar cutar Coronavirus a jiki na, na killace kai na. Kuma dukkan aikin gwamnati zai ci gaba da gudana.

“Ina barar addu’ar ku.”

Akeredolu ya zama gwamna na hudu da suka kamu da cutar Coronavirus.

Akwai Bala Mohammed na Bauchi, Nasiru El-Rufai na Kaduna da Seyi Makinde na Oyo.

Sannan kuma Gwamnan Ebonyi na can a killace, bayan an samu ‘yar sa dauke da cutar Coronavirus.

Akeredolu na shirin sake tsayawa takarar zarcewa karo na biyu, karkashin APC a zaben gwamnan Ondo da za a yi cikin watan Oktoba.

Idan ba a manta ba, a karshen wannan makon ne iyalai da ‘yan uwan marigayi Abiola Ajimobi suka yi jana’izar marigayin.

Marigayi Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo ne kuma zaɓaɓɓen sanata a majalisar dattawa dake wakiltar Shiyyar jihar Oyo.

Ya rasu bayan fama da Korona da yai a wani asibiti dake Legas.

Share.

game da Author